Ginin hedkwatar Media Trust sabon kalubale ne – Shugaban Kamfanin

Shugaba kuma Babban Jami’in Zartarwa na Kamfanin Media Trust Limited Malam Kabiru A. Yusuf ya ce ginin hedkwatar kamfanin mai hawa shida da ke Gundumar Utako a Birnin Tarayya Abuja da aka kammala babban ci gaba ne, kuma sabon kalubale ga kamfanin. Shugaban ya bayyana haka ne a jawabinsa wajen bikin shekara-shekara don karrama wadanda […]

Ginin hedkwatar Media Trust sabon kalubale ne – Shugaban Kamfanin
Ginin hedkwatar Media Trust sabon kalubale ne – Shugaban Kamfanin

Shugaba kuma Babban Jami’in Zartarwa na Kamfanin Media Trust Limited Malam Kabiru A. Yusuf ya ce ginin hedkwatar kamfanin mai hawa shida da ke Gundumar Utako a Birnin Tarayya Abuja da aka kammala babban ci gaba ne, kuma sabon kalubale ga kamfanin.
Shugaban ya bayyana haka ne a jawabinsa wajen bikin shekara-shekara don karrama wadanda suka shafe shekaru suna aiki da wadanda suka nuna hazaka da gaskiya da rikon amana a wajen aiki.
Ya ce: “A daidai lokacin da shugabannin gudanarwa da ma’aikatan ke farin cikin samun sabon muhallin gudanar da ayyukansu a wannan sabuwar hedkwata, to kada fa su dauka cewa kamfanin ya kai gaci, illa dai akwai bukatar su kara kwazo don a samu kaiwa ga nasara. Kudin tafiyar da wurin ya karu matuka, tunda aka dawo ginin.”
Ya ce duk da cewa jaridun Kamfanin Media Trust na cikin manyan jaridu uku ko hudu na kasar nan, sai dai manufar kamfanin ita ce samar da jaridu wadanda kimar darajarsu ta yi daidai da manyan jaridun duniya.
Ya ce, kamfanin ya dauki sababbin ma’aikata a cikin gida da wajen kasar nan “saboda ba mu da tabbacin cewa ma’aikatan da muke da su ko manyan jami’an gudanarwa suna da cikakkiyar kwarewa da gogewar da ake bukata don daga kimar kamfanin zuwa inda ake bukatar cimmawa.”
Ya taya wadanda suka samu kyaututtuka a matikai daban-daban murna, inda ya ce kamfanin zai ci gaba da bayar da lada ga wadanda suka nuna kwazo a aiki da tabbatar da gaskiya, al’amuran da daukacinsu su ne jigo da manufofin kamfanin.  A cewarsa, za kuma a ci gaba bayar da ladar dadewa kan aiki, ga wadanda suka shafe shekara 10 ko fiye a kamfanin.
Biyu daga cikin ma’aikatan kamfanin da suka hada da Salihu Makera na jaridar Aminiya da Salisu Dabo na sashin kasuwanci, sun samu kyautar shugaban kamfanin kan nuna gaskiya wajen aiwatar da ayyukansu. Wannan kyauta dai tana dauke da ladar Naira dubu 250. Sai kuma kyautar nuna hazakar aiki wadda aka ba wakilin jaridar Daily Trust na Jihar Yobe, Hamisu Kabir Matazu da Charles Mere na sashin tallace-tallace da ke Legas. Kuma daya daga cikin ma’aikatan kamfanin ya samu kyautar shafe shekara 15 yana aiki, yayin da saura suka shafe shekara goma-goma.