Ginshikin ci gaban tattalin arziki ya kafu – Kwararre
Wani mai fashin baki kan harkokin musayar kudi, Lookman Otunuga ya ce ginshikan da za su sanya Najeriya ta fara ganin bunkasar tattalin arziki a shekarar 2019 sun riga sun kafu. Otunuga ya yi wannan furuci ne a wata ganawa ta keke-da-keke da wadansu zababbun manema labarai a Legas a karshen makon jiya don duba […]
Wani mai fashin baki kan harkokin musayar kudi, Lookman Otunuga ya ce ginshikan da za su sanya Najeriya ta fara ganin bunkasar tattalin arziki a shekarar 2019 sun riga sun kafu.
Otunuga ya yi wannan furuci ne a wata ganawa ta keke-da-keke da wadansu zababbun manema labarai a Legas a karshen makon jiya don duba yadda lamura suka kasance a zango na biyu na shekarar da ta gabata.
Ya ce “Tashin farashin kayayyaki yana raguwa cikin sauri kuma musayar kudin kasashen waje tana daidaita. Muna son ganin wani babban mataki da gwamnati za ta dauka na bunkasa tattalin arziki da shirin farfado da shi.”
Ya bayyana cewa daya daga cikin abubuwan da za su taimaka ga ci gaba shi ne tallafa wa kanana da matsakaitan masana’antu.
Da yake bayani dangane da bunkasar tattalin arziki, Otunuga ya ce “Abu ne mai sauki mutum ya kushe Najeriya amma idan ka fadada tunani ba Najeriya ce kadai kasar da ke fuskantar kalubale ba, wasu kasashen duniya har da Amurka da China su ma ba su tsira ba”.
Ya ce yayin da tattalin arzikin duniya ke fuskantar koma-baya haka ma Najeriya kamar sauran kasashe za su ci gaba da fuskantar kalubale.
Ya bayyana cewa wasu kalubalen daga waje za su yi tasiri ga tattalin arzikin Najeriya saboda ba shi kadai ba ne.
“Kodayake musayar kudi ta daidaita, tattalin arzikin Najeriya ya dogara kacokan kan man fetur saboda haka akwai bukatar a ci gaba da kokari kan dogaro da wasu bangarori na tattalin arziki ta hanyar sanya jari mai yawa a harkokin noma,” inji shi.
Matakin Gwamnan Bankin CBN zai yi tasiri ga jarin kasashen waje na kai- tsaye
Otunuga ya bayyana cewa matakin canja ko ci gaba da Gwamnan Bankin CBN zai yi tasiri kan masu zuba jari daga kasashen waje.
Ya ce “Barin Emefiele kan matsayinsa yana nuna alamar ci gaba tare da cire duk wata fargaba sannan sauya Gwamnan zai kawo rashin tabbas. Tun 1999 babu Gwamnan Bankin CBN da ya yi fiye da zango daya a mukaminsa, akwai hanyoyi biyu da za mu kalli haka, idan muka kalli yadda Gwamnan Bankin CBN ya tsaya, hakan na nuna ci gaba bisa la’akari da abin da ke faruwa.
“Ci gaban zai cire rashin tabbas saboda yana daya daga cikin abubuwan da za su yi tasiri kan zuba jari na kai-tsaye daga kasashen waje amma idan aka nada wani Gwamnan Bankin CBN din, hakan zai iya kawo rashin tabbas saboda ba mu san abin da zai yi ba. Ba wanda ya san abin da zai faru. Shin sabon Gwamnan zai bar Naira ta samu ’yanci? Shin sabon Gwamnan zai iya daukar mataki na karya darajar Naira nan take ba kamar yadda aka yi tsammani ba?,” inji shi.
Otunuga ya ce akwai tambayoyi masu yawa da kuma rashin tabbas.
Batun fitar Ingila daga Tarayyar Turai kaifi biyu ne na takobi ga Najeriya da Afirka
Da yake tattauna batun tasirin matakin ficewar Ingila daga Tarayyar Turai da gwamnatin Firayi Ministar Birtaniya Theresa May ke tattaunawa ko yarjejeniya a kai , Otunuga ya ce “Batun ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai tamkar kaifi biyu ne na takobi saboda akwai hanyoyi masu yawa da za mu kalle shi. Yadda ita kanta Theresa ke kallon matakin ficewar tana yi masa kallon darewar kasar Birtaniya inda kasashen za su samu ’yancin kansu na yi wa tsarin kasuwancinsu garambawul.
“Tambayar ita ce yadda tattalin arzikin Birtaniya zai kasance in ma ficewar ta auku kamar yadda kake ganin lamarin, za a ki karbar ra’ayin Theresa May kuma hakan zai bude kofar yiwuwar gudanar da sababbin zabubbuka. Wannan daya ne daga cikin abubuwan da za mu sanya a zuciyarmu. Wani abu da za mu sa ranmu shi ne idan kuri’un ficewar Birtaniya suka kai ga batun ficewar hakan zai shafi darajar kudin kasar ta hanya mai kyau amma kuma kalubalen kasancewar kasar cikin rikicin ficewar kasar ba abu ne mai kyau ba ga kasar,” inji shi.
Ya ce “Idan Birtaniya ta makale cikin batun ficewar dukan tsare-tsaren da Theresa May ta shirya wa Nahiyar Afirka ba za su yiwu ba har sai Birtaniya ta fita daga batun ficewar. Ba mu san abin da zai faru ba a yanzu idan aka fadada doka ta 50 kuma muka samu kanmu amma idan batun ficewar ya kai karshen bana, dukan tsare-tsaren da Theresa May ta tanada don Nahiyar Afirka ba za su iya tabbata ba, har sai shekarar 2020 da shekarar 2021.”
“Amma idan Birtaniya ta yi nasarar ficewa daga Tarayyar Turai kuma ta farfado hakan abu ne mai kyau ga kasashen Nahiyar Afirka musamman idan Birtaniyar ta dawo cikin hayyacinta,” inji shi.
Dangane da sanya Kamfanin MTN a tsarin Hukumar Hada-Hadar Hannayen Jari
Da yake bayani dangane da sanya Kamfanin MTN cikin tsarin Hukumar Hada-Hadar Hannayen Jari, Otunuga ya ce yana da tabbacin hakan zai bunkasa kasuwar hannu jari da tattalin arziki baki daya.
Ya ce sanya kamfanin cikin kasuwar hada-hadar hannun jari mataki ne na sam barka a kasuwar hannun jarin.
Otunuga ya ce lamarin zai bunkasa kasuwar a karamin lokaci da kuma na dogon lokaci tare da hakan zai dogara ga yadda kasuwar ta kasance.
Babban Jami’in Kamfanin MTN, Mista Ferdi Moolman yayin tattaunawa da editocin hada-hadar kudi a Legas ya ce manyan kamfanonin sadarwa bayan dagewar da aka yi ta yi yanzu za su shiga cikin kasuwar hannun jarin kasar nan kafin watan Mayun bana.
Ya ce sanya su ciki zai zama ta fuska biyu yayin da kamfanin zai shiga cikin jerin kamfanonin da ake hada-hadar hanun jarinsu sannan daga bisani zai sayar da jarinsa ga jama’a.
Matakin Kamfanin MTN na shiga kasuwar hannun jari ya taso ne bayan bayyana hada-hadarsa a karshen watan Disamban bara, inda ya samu ribar Naira biliyan 453.1 kafin cire kudin ruwa da haraji da faduwa a barar.
Moolman ya ce kamfanin yana ta yin shirye-shirye don tabbatar da ganin shigarsa cikin kasuwar hannayen jarin ba ta samu matsala ba.
“Muna ta yin shirye-shirye don tabbatar da ganin shigarmu ta samu nasara. Wannan shi ne daya daga cikin dalilan da suka sanya aka samu dan tsaiko na shigarmu kasuwar amma ga alamu na yi imanin za mu yi rajista kafin watan Mayun bana,” inji shi
Matakin sayar da hannun jarin kamfanin na daga cikin yarjejeniyoyin da suka danganci tarar Dala biliyan biyar da digo biyu da aka sanya wa kamfanin kan layukan da ba su da rajista.
Amincewar kamfanin ya shiga kasuwar hannayen jarin kasar nan na daga cikin sasantawar da aka yi na rage tarar daga fiye da Naira tiriliyan daya a shekarar 2015 saboda kasa yi wa masu hulda da kamafanin rajista wanda ya kai na kimanin Naira biliyan 330.