Girgizar kasa: Morocco ta ayyana makokin kwana 3

Sarki Mohammed VI ya ba da umarnin kafa kwamitin ba da agaji da tallafi da kuma kulawa ga wadanda lamarin ya shafa

Girgizar kasa: Morocco ta ayyana makokin kwana 3

AL’ummar Morocco sun koma yi kaura zuwa wani dandali a binin Marrakesh bayan girgizar kasa mai karfin maki 6.8 da ta kasu mutum kusan 300 a daren 8 ga Satumba, 2023. (Hoto: Fadel Senna/ AFP).

Gwamnatin Morocco ta ayyana zaman makoki na kwana uku a sakamakon mummunar girgizar kasa da aka samu a kasar.

Hakan na zuwa ne a yayin da ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar ta sanar cewa yawan wadanda suka rasu a girgizar kasar ya haura 1,300, wasu 1,220 kuma na cikin mawuyacin hali daga cikin mutum 1,832 da suka samu rauni a iftila’in.

Bayan wani taron gaggawa kan girgizar kasar, Fadar Sarki Mohammed VI ta sanar cewa za a yi kasa-kasa da tutar kasar a duk gine-ginen gwamnati.

Sarkin ya ba da umarnin kafa kwamitin aiki da cikawa domin ba agajin da tallafi da kuma kulawa a wadanda lamarin ya shafa, musamman kananan yara da marayu.

Kwamitin zai kuma samar da matsuguni da kayayyakin bukatar yau da kullum ga mutanen da suka rasa muhallansu, tare da kuma sake gina wuraren da suka rushe.

Haka kuma, sarkin ya ba da umarnin bude asusu na musamman a babban bankin kasar domin bayar da tallafi.Girgizar kasar daren Juma’a ita ce mafi muni a baya-bayan na a birnin Marrakesh, da ma kasar, wajen karfi da kuma yawan wadanda abin ya shafa.