Girgizar kasa: Ya rage na Morocco ta nemi taimakonmu —Faransa

Catherine Colonna na amsa tambayoyi kan dalilin da ya sa ba a saka Faransa cikin ƙasashen da ake kira da su taimaka ba.

Girgizar kasa: Ya rage na Morocco ta nemi taimakonmu —Faransa

Girgiar kasar mai karfin maki 6.8a Marrakesh ta ya ajalin daruruwan mutane. (Hoto: FADEL SENNA / AFP)

Ministar harkokin wajen Faransa ta nanata cewa ya rage ga Maroko ta nemi taimakon Faransa don taimaka mata wajen shawo kan mummunar girgizar kasar da ta faɗa mata.

Catherine Colonna na amsa tambayoyi kan dalilin da ya sa ba a saka Faransa cikin ƙasashen da ake kira da su taimaka ba.

Zuwa yanzu an tabbatar da mutuwar mutum 2,681 sakamakon girgizar ƙasar ta faru ranar Juma’a da dare.

Duk da dai cewa jami’an Faransa sun sha musanta cewa akwai wata ɓaraka a alaƙrsu da Maroko, an kwashe watanni babu wanda ke riƙe da muƙamin jakadan Maroko a Faransa.

Haka nan, an sha ɗage ziyarar da Shugaba Emmanuel Macron zai kai birnin Rabat.