Girgizar kasar Turkiyya: An ceto mutum 3 da rai bayan shafe kwana 13 ba ci, ba sha
Mutanen sun shafe sama da sa’o’i 296 ba ci, ba sha
Masu aikin ceto a kasar Turkiyya a ranar Asabar sun zakulo mutum uku da ransu a cikin baraguzai bayan shafe kwana 13 da mummunar girgizar kasar da ta halaka dubban mutane a kasar.
Kafafen yada labaran kasar sun ce daga cikin wadanda aka ceto din, har da wani karamin yaro, amma daga bisani daya daga cikinsu ya ce ga garinku nan.
- 2023: Na fasa takarar Gwamnan Kano a LP, na koma wajen Tinubu – Bashir
- Mata 4 na mutum 1 sun haihu rana daya a sansanin ’yan gudun hijira
Sai dai kafar ba ta yi cikakken bayani a kan hakan ba.
Amma wani dan jarida da ke aiki da gidan talabijin na NTV ya ce daya daga cikin wadanda aka ceto din ya rasu daga bisani lokacin da aka kai su asibiti.
Gidan talabijin din ya uma nuna hotunan ma’aikatan ceto suna sanya mutanen a gadajen ceto bayan sun shafe saman da sa’o’i 296 a cikin baraguzai.
Girgizar kasar mai karfin 7.8 dai ta fada wa kasashen Turkiyya da Siriya ne shida ga watan Fabrairu, inda ta halaka sama da mutum 43,000 ta kuma raba miliyoyi da muhallansu.
Ma’aikatan ceto dai sun yi ta aikin ceto mutanen da gine-ginen suka danne a daidai lokacin da kasar ke fama da tsananin sanyi.
Ko a ranar Juma’a, sai da ma’aikatan ceton na Turkiyya suka ceto wata mata mai shekara 45 ita ma da ranta. (AFP)