Girija Srinibas: ’Yar shekara 19 mai jikin ’yan shekara 2

Da farko idan mutum ya dubi Girija Srinibas, zai ce yarinya ce karama wadda ba ta wuce shekara biyu da haihuwa ba. Amma a zahiri yarinyar tana da shekara 19 ne da haihuwa a bana, sai dai ba a yawancin lokuta za ka same ne a goye a bayan mahaifiyarta.  Yarinyar wadda take zaune ne […]

Girija Srinibas: ’Yar shekara 19 mai jikin ’yan shekara 2
Girija Srinibas: ’Yar shekara 19 mai jikin ’yan shekara 2

Da farko idan mutum ya dubi Girija Srinibas, zai ce yarinya ce karama wadda ba ta wuce shekara biyu da haihuwa ba. Amma a zahiri yarinyar tana da shekara 19 ne da haihuwa a bana, sai dai ba a yawancin lokuta za ka same ne a goye a bayan mahaifiyarta. 

Yarinyar wadda take zaune ne a birnin Bangalore na kasar Indiya, tana fama ne da wata lalura da ke hana girman kashi wadda ta haddasa kasancewa kamar karamar yarinya. Hakan ya sa ba ta wuce tsawon kafa biyu da rabi ba kuma nauyinta yake kilo 12, daidai da na yarinya ’yar shekara biyu.
Yarinyar ba za ta iya zama ba saboda kanta ya yi nauyi sosai kuma yakan rinjayi sauran jikinta. Har ila yau, ba ta iya daukar abin da ya fi nauyin kofin shayi da hannunta. Bugu da kari, likitoci sun ce idan ta ce za ta juya wuyanta cikin hanzari ta na iya samun karaya da kuma matsa wajen lumfashi.
Halin da take ciki yana nuni da cewa hatta kananan bukatunta ba ta iya biya ba tare da tallafin mahaifiyarta ba. Kodayake, Srinibas ba ta yi kasa a gwiwa ba saboda a yanzu haka ta yi nisa a koyon zane-zane. Ta bayyana wa jaridar Daily Mail da ke Birtaniya cewa tana koyon zanen ne saboda tana da fatan dogaro da kanta da kuma burinta ganin cewa a nan gaba ta dauki dawainiyar iyayenta.
Ta ce: “Ba na so kowa ya ji tausayina saboda na nuna wa kowa irin abubuwabn da zan iya yi.” Ta ci gaba da cewa maihaifiyarta na taimakonta wajen cin abinci da sauran bukatunta. Amma lokacin da nake aikin zane-zane ba na bukatar tallafi daga kowa. “Ina sayar da aikin zane-zane akalla guda shida, wanda yakai kudi rupees 8000 zuwa 10,000 (kimanin naira dubu 30 zuwa dubu 60).”