Girke-girken Azumi: Yadda ake yin Tsiren Dankali
Za a iya amfani da girkin namu na yau a matsayin abin buɗa-baki, da zarar an sha ruwa.

Yau a filin namu na Girke-girken Azumi za mu kawo muku yadda ake yin Tsiren Dankali.
Za a iya amfani da girkin namu na yau a matsayin abin buɗa-baki, da zarar an sha ruwa.
- Mahara sun yi basaja da kayan EFCC wajen sace mutum 10 a otal
- Sojoji sun ƙwato makamai a dajin Sambisa
Ga kayan hadin da ake bukata don yin girkin:
- Dankali Turawa
- Nikakken nama
- Man gyada
- Sinadarin ɗanɗano
- Kori
- Tyme
- Tafarnuwa
- Tsiken tsire
Yadda ake hada shi
A samu nikakakken nama sai a hada da kayan kamshi(kori, tyme da tafarnuwa) da sinadarin ɗanɗano.
Idan ya hadu sai a gutsira a fadada shi yadda zai yi falan-falan sai a ajiye shi a gefe.
Sannan a dauko dankali sai a fere shi, a yayyanka shi kamar kwabo.
Sai a dauko tsinken tsire a jera dankalin a jiki tare da hadadden nikakken naman.
Idan an sa dankali a jikin tsinken sai a dauko wannan nikakken naman a sa shi a jiki daidai fadin dankalin sannan sai a sake sa dankalin sai a sa naman.
Haka za a yi, har sai tsinken ya cika.
Amma a tabbatar dankalin da aka yanka ya kasance guda daya, ma’ana sai kin gama da guda daya, sannan za a sake yanka wani don kada ya hargitse wajen dankalin a jikin tsinken.