Girki na musamman domin Babbar Sallah
Hadin abinci mai kayatarwa da gamsarwa kuma ya fi wanda aka saba ci da sallah
A duk sadda ake shirye-shiryen Sallah, uwar gida kan so yin girki na musamman da zai kayatar ya kuma gamsar, in da hali ma girkin ya darar abin da ake gani tamkar abincin jiya-i-yau.
Mun yi tanadin yadda za ki yi girkin shinkafa mai kasa da kuma sos din kaza domin kaytar da iyalai da abokan arziki a lokacin bukukuwan Sallah.
Ku ci gaba da bin mu don samun salon girki iri-iri a wannan shafi, amma yanzu ka kwatancen girkinmu na wannan karon:
(1) Shinkafa mai Karas
Kayan hadi:
Shinkafa
Karas
Yankakken attarugu
Albasa
Tafarnuwa
Danyar citta
Kayan kanshi
Farin mai
Sinadarin dandano
Yadda ake yi:
Ki samu shinkafarki ki tafasa ta ki tace da kwando, sai ki ajiye a gefe.
Sai ki yanka karas mai yawa kanana, sannan sai ki tafasa ki tace ki ajiye a gefe.
Ki dauko tukunya ki zuba man girki a ciki sai ki zuba jajjagen citta da tafarnuwa a ciki sai ki soya shi sama-sama.
Sannan ki kawo albasa ki zuba ki, ci gaba da juyawa.
Idan ya soyu sama-sama sai ki dauko shinkafarki wacce ta tsane sai ki zuba a ciki.
Sannan sai ki zuba sinadarin dandano da kayan kanshi a ciki sai ki juya.
Daga nan sai ki dauko tafasasshen karas dinki ki zuba a ciki.
Sai ki dauko attarugu ki zuba a kai domin ya ba shi kanshi na musamman.
(2) Sos din kaza
Kayan hadi:
Kaza
Kayan kanshi
Sinadarin dandano
Attarugu da tumatir
Albasa
Tafarnuwa da danyar citta
Farin mai
Koren tattasai
Yadda ake yi:
Uwargida za ki samu kaza ki yayyanka ta, sai ki tafasa ta da albasa da danyar citta da tafarnuwa da gishiri da sinadarin dandano.
Idan ta dahu sai ki ajiye a gefe. Sannan sai ki yayyanka albasa da attarugu da tumatir da koren tattasai sai ki ajiye su a gefe.
Daga nan sai ki dauko tukunya ki zuba farin mai a ciki ki zuba jajjagaggiyar citta da tafarnuwa a cikin man sai ki dan soya sama-sama.
Sannan sai ki dauko yankakkiyar albasarki ki zuba, sai ki juya.
Daga nan sai ki kawo yankakkun attarugu da tumatir ki zuba a kai.
Sai ki kawo kayan kanshi da sinadarin dandano ki zuba ki jujjuya.
Bayan haka sai ki dauko kazar nan ki zuba a kai, ki jujjuya.
Idan kika gama sai ki dauko yankakken koren tattasanki ki zuba a ciki, sannan ki sa murfin tukunyar ki rufe. Sai ki rage wuta.
Idan kika duba kika ga ya yi shi ke nan sai ki sauke.
Sai a ci wannan sos din kazar da shinkafa mai karas.