Girkin ‘Couscous’ da naman akuya

By Amina Abdullahi, Yola Barkanmu da warhaka tare da fatan kuna nan lafiya. Yaya shirin Ramadan? Allah Ya nuna mana lafiya. Ina fata Uwargida za su taka rawar gani wajen hada nau’ukan girke-girke domin farantawa masu gida rai idan Ramadan ya gabato. Yanzu lokaci ya yi da za a fara yin gwajin irin girke-girke da muke […]

Girkin ‘Couscous’ da naman akuya

By Amina Abdullahi, Yola

Barkanmu da warhaka tare da fatan kuna nan lafiya. Yaya shirin Ramadan? Allah Ya nuna mana lafiya. Ina fata Uwargida za su taka rawar gani wajen hada nau’ukan girke-girke domin farantawa masu gida rai idan Ramadan ya gabato. Yanzu lokaci ya yi da za a fara yin gwajin irin girke-girke da muke kawo muku domin kwarewa da kuma samun irin dandanon da ya kamaci kowane girki.  A yau na kawo muku yadda ake girka ‘Couscous’ da naman akuya. A ci dadi lafiya.

Abubuwan da za a bukata:

• ‘Couscous

• Naman Akuya

• Attarugu

• Albasa

• Magi

• Tafarnuwa

• Tumatir

•Citta

• Bota

•Man gyada

• kori

Hadi:

A dora ruwa a tukunya har sai ta tafasa sannan a zuba garin couscous ana gaurayawa da cokali har sai ruwan ya dan haura kadan a sama sannan a rage wuta sai a rufe na tsawon mintuna biyu zuwa uku sannan a debo bota a zuba a sama sai a sake gaurayawa da shi. Sannan a sauke.

A sulala naman akuya da albasa da gishiri har sai ya yi laushi sannan a sauke a ajiye a gefe. A dora tukunya a wuta sannan a zuba yankakkiyar albasa da yankakken tumatir da kuma jajjagen tafarnuwa da attarugu sannan a cigaba da juyawa har sai ya soyu.

Sai a debo magi da kori da garin citta a zuba sannan a zuba sulalen naman a cikin hadin tare da zuba romon naman kadan sannan a rufe. Bayan mintuna uku sai a sauke a zuba couscous a kwano sannan a zuba miyar naman akuya a gefe hade da lemun kwalba mai sanyi.