Girkin koda
Assalamu alaikum Uwargida yaya yara? Tare da fatan ana lafiya. A yau na kawo muku yadda ake girka koda. Akwai hanyoyi da dama wadanda mata ke sarrafa koda. Walau a gasa ko a girka. Nawa salon girkin daban yake. Don haka yana da kyau a kasance an karanta wannan shafin domin gano sirrin girki da […]
Assalamu alaikum Uwargida yaya yara? Tare da fatan ana lafiya. A yau na kawo muku yadda ake girka koda. Akwai hanyoyi da dama wadanda mata ke sarrafa koda. Walau a gasa ko a girka. Nawa salon girkin daban yake. Don haka yana da kyau a kasance an karanta wannan shafin domin gano sirrin girki da kuma canza salon girki a kodayaushe, domin yara su rage kwadayi a makwafta.
Abubuwan da za a bukata
•koda
•Albasa
•Tumatir
•Garin tafarnuwa
•Magi kori
•Garin citta
•Attarugu
• Man gyada
• Koren tattasai
Hadi
A wanke koda ta fita tas. Sannan a yayyankata kanana, sai a sanyata a cikin tukunya tare da zuba mata ruwa kadan. Sannan a rufe. Idan ya fara nuna sai a yayyanka albasa da yawa a ciki da zuba yankakken tumatir da magi da garin tafarnuwa da kuma garin citta kadan sosai. Sannan a rage wuta sai a shiga gaurayawa. A zuba man gyada kadan sai a cigaba da juyawa har sai albasa da tumatar da kuma attarugu sun nuna. Sannan a kwashe a sanya a kwano. Sai a yayyanka danyen albasa da koren tattasai a zuba a kan kodar domin kawata girkin.
Za a iya cin wannan girkin da dafadukar shinkafa ko kuma farar shinkafa da jus din lemun zaki. A ci dadi lafiya.