Girkin kwai a cikin kwai

Barkanmu da warhaka uwargida, tare da fatan alheri, kuma ana cikin koshin lafiya. Ba zan gaji da gaya muku cewa, yana da kyau a  koyi nau’ukan girki  domin inganta girki da kuma gyara zamantakewar uwargida da maigida. Don haka ne a yau na kawo muku wannan girki na kwai a cikin kwai. Na san za […]

Girkin kwai a cikin kwai
Girkin kwai a cikin kwai

Barkanmu da warhaka uwargida, tare da fatan alheri, kuma ana cikin koshin lafiya. Ba zan gaji da gaya muku cewa, yana da kyau a  koyi nau’ukan girki  domin inganta girki da kuma gyara zamantakewar uwargida da maigida.
Don haka ne a yau na kawo muku wannan girki na kwai a cikin kwai. Na san za a yi mamakin irin wannan girki ko kuma a ce yaya kamannin wannan girkin zai kasance. Kada a gaji da karanta shafin girke-girkenmu domin fahimtar sirrin girki da sarrafa su da kuma yadda ake hada su. A sha karatu lafiya:
Abubuwan da za a bukata
•         kwai
•         Magi
•         Hanta
•         Kori
•         Albasa
•         Attarugu
•         Man gyada
•         Leda

Hadi
A samu kwai kamar guda biyar. Sai a wanke su da soso da sabulu. Sannan a kula domin kada kwan ya fashe. Idan an gama wankewa, kuma an dauraye sai a ajiye shi a gefe. A wanke hanta sannan a sulala shi da albasa ya nuna ya yi laushi sosai. Sannan a yayyanka shi kanana sosai a ajiye a gefe. A jajjaga attarugu, shi ma a ajiye a gefe. A yayyanka albasa kanana sosai a ajiye.
A samu kwan nan da aka wanke a dan bantare samansu kadan ba tare da an fasa bawon ba. Sannan sai a zazzage ruwan a kwano. A zuba yankakkiyar hantar da albasar da jajjagaggen attarugu da magi sannan sai a kada su. A zuba magi da kori kadan. In ana cin tafarnuwa ma sai a dan zuba garinta kadan, sannan a sake kada kwan.
Bayan haka, sai a diga man gyada kadan a cikin kwan sannan a zuba wannan ruwan kwan da aka yi wa hadin a bawon kwan a saka a leda a kulle shi, yadda ruwan kwan ba zai zuba ba.
A dora ruwa a wuta. Bayan ruwan ya tafasa, sai a zuba wannan kullallen kwan a cikin ruwa. Sai a rufe a jira na tsawon minti takwas. Sannan a saka kwan a ruwan sanyi sai a bare. Za a iya cin wannan kwan da farar shinkafa, ko kuma da dafa-dukan shinkafa.