Girkin manyan gobe: farfesun kifi da kayan lambu

Barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan filin namu na girke-girke. Ko kun taba zama domin yin tunanin irin girkin da ya dace da manyan gobe musamman a wannan lokaci na sanyi? To idan ba a taba yi ba, a kasance tare da mu a shafin girke-girke na jaridar Aminiya a kowane mako […]

Girkin manyan gobe: farfesun kifi da kayan lambu

Barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan filin namu na girke-girke. Ko kun taba zama domin yin tunanin irin girkin da ya dace da manyan gobe musamman a wannan lokaci na sanyi? To idan ba a taba yi ba, a kasance tare da mu a shafin girke-girke na jaridar Aminiya a kowane mako domin samun kayatattun girke-girke da za su sanya manyan gobe cin abinci sosai.

Abubuwan da za a bukata

•        Kifi

•        Karas

•        Albasa

•        Kabeji

•        Ganyen kori

•        Magi

•        Nikakken masoro

•        Attarugu (ga masu bukata)

•        Man zaitun

•     Citta

Hadi

A samu gasasshen kifi tarwada ko karfasa, a wanke shi sosai a ajiye ya sha iska sannan a bare bawonsa. Sannan a yayyanka shi kanana.

Bayan haka, sai a dora man zaitun a wuta sannan a yayyanka albasa ta dan soyu kadan sannan a zuba ruwa da yankakken kifin da garin nikakken masoro da yankakken ganyen kori da magi da dakakkiyar citta.

Idan kifin ya fara tafasa sai a zuba yankakken kabeji a ciki sannan a jajjaga attarugu a zuba (ga masu cin attarugu).

Sai a jira na tsawon mintuna biyar sannan a sauke hade da romonsa.

Wannan irin farfesun kifin na warkar da murar yara da kuma kare su daga tarin lokutan sanyi. A ci dadi lafiya!