Girkin nadadden nama
Uwargida barkanmu da warhaka tare da fatan alheri da kuma fatan ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake girka nadadden nama. Yana da kyau Uwargida ta kasance mai tsabtace jiki da kuma iya sarrafa girki daban-daban. Don haka dole ne mace ta dage wajen taka rawar gani a harkar girki tare […]
Uwargida barkanmu da warhaka tare da fatan alheri da kuma fatan ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake girka nadadden nama. Yana da kyau Uwargida ta kasance mai tsabtace jiki da kuma iya sarrafa girki daban-daban. Don haka dole ne mace ta dage wajen taka rawar gani a harkar girki tare da koyon kowane irin salon girki. Nadadden nama dai ana iya cin sa a kowane lokaci walau da safe ko da rana ko kuma da dare.
Abubuwan da za a bukata:
• Namar karamar dabba
• Man zaitun
• Garin tafarnuwa
• Garin citta
• Gurji
• Garin masoro (black pepper)
• Barkono
• Kori
• Latus
Hadi:
A samu danyen naman rago wanda bai cika maiko ba. Sannan a yayyanka da fadi sosai kamar tabarma. Sannan a samu kwano a zuba garin tafarnuwa a ciki sannan a zuba garin masoro da barkono da garin citta da kori sannan a zuba man zaitun sai a kwaba sosai.
A yayyanka gurji sala-sala a ajiye a gefe. A samu cokali ana dibar hadin man zaitun ana shafawa a kan naman. A zuba hadin isasshe sannan a dauko salan gurji ko latus a shimfide shi a kai sannan a yi masa nadin tabarma. Sai a dauko tsinken sakace hakori ‘toothpick’ a soke naman da shi yadda nadin ba zai warware ba sannan a saka a na’urar gashi a gasa na tsawon minti 30 zuwa 35.