Girkin Sallah na musamman
Yana da muhimmacin gaske mu dinga kokarin kyautata abinci, tare da canja shi lokaci zuwa lokaci. Kazalika lokutan bukukuwan sallah lokaci ne na sanya farin ciki a zukatan al’umma daban-daban, tun daga yaran gida da dangi, da ma’aikatan gida, har da makota. In dai da hali, za a samu lada. Domin taya murnar zagoyowar ranar […]
Yana da muhimmacin gaske mu dinga kokarin kyautata abinci, tare da canja shi lokaci zuwa lokaci.
Kazalika lokutan bukukuwan sallah lokaci ne na sanya farin ciki a zukatan al’umma daban-daban, tun daga yaran gida da dangi, da ma’aikatan gida, har da makota. In dai da hali, za a samu lada.
Domin taya murnar zagoyowar ranar sallah mun tanadi girke-girke guda 2 da miya 2:
1. Tuwon Shinkafa
2. Funkaso
Miya kuma
1. Taushe
2. Agushi
1. Tuwon Shinkafa
Za ki dora ruwa a tukunya yai zafi, ki wanke shinkafar tuwo ki zuba ta a ciki. Har sai ta dahu luguf.
Ki latsa Shinkafar da hannunki ki tabbatar ta yi tibis tibis.
Sai ki sa muciya ki tuka ta da kyau. Ki rage wuta, ki bar ta zuwa wani lokaci ta turara.
A bar ta, ta turara sosai a hankali. Sai ki kwashe. Ki malmala da koko ki dinga sakawa a kwanuka.
2. Miyar Agushi
Za ki zuba mai, ki soya shi da albasa. Idan ya yi zafi, ki zuba markadadden kayan miya.
Bayan sun soyu ki zuba ruwan nama, wankakken busasshen kifi, albasa, sinadarin dandano.
Idan ya tafasa, sai ki samu roba ki zuba agushi ki jika shi da ruwan zafi.
Ki juye shi cikin miyarki dake tafasa. Ki juya sosai. Kuma ki sa kayan kamshi.
Idan agushin ya hadu, sai ki zuba wankakken ganyen ugu . Ki juya, kuma ki dandana ko akwai bukatar kara kayan dandano.
Dakikoki kadan sai ki sauke miyar ki daga wuta.
3. Funkaso
Abubuwan da ake bukata na kayan hadin Funkaso wanda wasu ke masa kirari da “babban girki, kowa ya ci sai ya sha ruwa” sun hada da;
Fulawa Rabin kwano
Alkama Rabin kwano
Yis cokali 2
Gishiri daidai.
Yadda Ake Yi:
Za a hada Fulawa da yis da gishiri, sai a zuba ruwa a kwaba, amma fa ka da yayi ruwa, ya zama kamar kwabin fanke.
Sai a dora mai yai zafi, a shafa mai (mara/zafi) a dinga shafa shi a bayan marar kwashe tuwo, ana sa kwabin a fadada shi. Sai a dinga sawa a mai ana soyawa.
4. Miyar Taushe
Za ki soya markadadden kayan miya, sai ki zuba ruwa da daddawa. Ruwan ya dan haura yadda kike bukatar miya. Domin miyarki ta dahu sosai .
Idan ta tafasa, sai ki sa dakakkiyar gyada ki juya. Ki zuba sinadarin dandano, da gishiri, da albasa, da garin citta, da kuma kanin fari.
Bayan jimawa ta dahu, sai ki zuba yankakken alayyaho (wankakke).
‘Yan dakikoki kadan ganyen ba a barin sa yai ta shan wuta. Sai ki kashe wuta ki juye miya.
Da fatan za a yi Sallah lafiya.