Girkinki ’yancinki
Sanin kowa ne girki shi ne babban makamin mallake miji, kuma matan mu na kokari matuka wajen ganin sun inganta abincin su na yau da kullum kai har ma da sauran kayan marmari. Da yawa daga cikin mata suna kokarin ganin sun yi amfani da gwargwadon abin da Allah Ya hore wa mazajen su na […]
Sanin kowa ne girki shi ne babban makamin mallake miji, kuma matan mu na kokari matuka wajen ganin sun inganta abincin su na yau da kullum kai har ma da sauran kayan marmari.
Da yawa daga cikin mata suna kokarin ganin sun yi amfani da gwargwadon abin da Allah Ya hore wa mazajen su na chefane wanda wasu har kara wa suke yi daga cikin jakar su yayin da wasu ke yin dabaru a yayin da maigidan ya tashi ba wadatattun kudin chefanen ta hanyar sarrafa kayan abincin ya ba da dandano mai dadi ko a samu canjin kalar abincin don a samu canji daga wanda aka saba ci yau da kullum.
Amma a wani bangaren wasu matan ba jawo hankalin mazajen ne a gaban su ba ta hanyar inganta abincin inda suka buge da ta yaya za su tara kudi ta hanyar kudin cefanen da ake ba su ko da kuwa maigidan zai koka a kan dandanon abincin.
Za ka samu wasu matan ba su da wata dabara da za su yi don kirkiro da wata sana’a a cikin gidajen su komai kankantar ta don biyan bukatun su na yau da kullum, amma za ka same su suna gogayya da manyan mata ma’aikata ko ‘yan kasuwa wajen yin adashin wata-wata ko makamancin haka.
Duk da a wani bangaren akwai laifin wasu mazajen da ba su iya biya wa matan su wasu bukatun su har sai sun kirkiri wani gibi da za su cire daga cikin kudin cefanen, kai ta kai ga wasu magidantan suna rungume hannuwan su ne kawai su bar mata da daukar dawainiyar yin cefanen wanda hakan ke tursasa masu yin ayyukan karfi da sanya ‘ya’yan su yin bara ko roko ko kuma tallace-tallace.
Koma me kenan, a nan, ina magana ne a kan mazajen da suka tsare wa matan su dukkanin hakkokin su amma sai su rika cire wani kaso daga ciki suna tarawa ba tare da sun yi yarjejeniya ba, ko ya amince duk abin da ya ba ki in ya yi saura naki ne.
Ko shakka babu aikata hakan zai dakusar miki da mutunci da kimar ki ga maigida don kuwa komai dadewa sai ya gane da kudin da kika shiga wannan adashi kai ko bai yi miki magana ba ai ya san samun ki, ya san ko za ki iya tattara wadannan kudade ko ba za ki iya ba.
A nan abu mai mahimmanci shi ne, a matsayin ki na uwargida ki kirkiri wata sana’a kamar yadda na ambata a sama domin ki biya bukatunki wanda ba sai mace ta dogara ga namiji ba ko ta rika yawan rokon sa wanda shi ma rokon na zubar da kimar mace ga mijin ta.
A karshe ina ba magidanta shawara da su kula da bukatun matansu wanda ba su taka kara suka karya ba, domin kuwa maza na ganin cewa ai ba rashin ci, ba rashin sha, amma sai ka samu mace Naira biyar da za ta ba da don a sayo mata ruwa ba ta da ita ko kuma a ce da za ta yi ba ki ba ta da abin da za ta ba ko da yaro ne balle a yi maganar su katin waya da sauran su.
A bangaren matan kuma kamar yadda na ambata a sama kar a ce mace ta dogara a kan komai sai mijin ta ya yi mata ko kuma ta rika tsakurar dan abin da yake ba ta na cefane wanda na ce zai rage mata kima a wajen sa.
Da fatan dukkanin mu kama daga magidantan har matan za mu gyara don a samu walwala da jin dadi a gidajen auratayyar mu.
Sanusi Hashim Abban Sultana
Ya rubuto ne daga Jihar katsina.
08065507271