‘Girman kai rawanin tsiya’(1)

Barkanmu da warhaka Manyan gobe tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya. Allah Yasa haka amin. A yau na kawo muku labarin ‘girman kai rawanin tsiya’. Labarin ya kunshi yadda ji da kai ke janyo masifa. A sha karatu lafiya. Akwai wani makeri ne a wani kauye mai suna tubus. Idan ya kera […]

‘Girman kai rawanin tsiya’(1)
‘Girman kai rawanin tsiya’(1)

Barkanmu da warhaka Manyan gobe tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya. Allah Yasa haka amin. A yau na kawo muku labarin ‘girman kai rawanin tsiya’. Labarin ya kunshi yadda ji da kai ke janyo masifa. A sha karatu lafiya.

Akwai wani makeri ne a wani kauye mai suna tubus. Idan ya kera abu, abin na matukar yin kyau. Don haka ya samu karbuwa a aikinsa kuma yana samun masu sayen kayansa.
Rannan sai ya samu labarin cewa akwai wani dodo dake jin haushinsa don haka zai zo ya dau ransa nan da makwanni biyu.
Sai makerin ya yi tunanin yadda zai yi. Can sai ya tuna! Ya dauko wani hotonsa ya kera gunki mai dai-dai tsayinsa guda goma sha biyar. Tare da sanya wa gumakan kaya irin nasa.
Da ranar zuwan dodon ta iso sai ya yi maza ya je ya tsaya a tsakanin gumakan ba tare da yin motsi ba. Dodo kuma ya aiki dan aike ne. dan aiken da ya kasa gane makeri sai ya koma ya gaya wa dodo. Abin yayi matukar batawa dodo rai. Sai dodo yaje da kansa.
Sai ya ce “haba makeri ai wannan gunkin bai keru da kyau ba domin an samu tangarda a wannan”. A maimakon makeri ya yi shiru, amma don ji da kai da son a sani sai ya fito ya ce “ nuna min inda na yi kuskure”. Dodo na ganinsa bai yi wata-wata ba sai ya fille masa kai.

Taku; Gwaggo Amina