Girman kai: Shawarwari ga matasa

A yadda duniya ta sukurkuce, babbar hanya wacce za ta kai mutum ga mafita, amma ba karya ba da gadara.

Girman kai: Shawarwari ga matasa

Masu yi wa kasa hidima

Kamar yadda kanun maudu’inmu ya nuna, za mu ba da wasu shawarwari ne na musamman ga matasanmu game da al’amuran rayuwa.

Kodayake ba zan mance ba, mun taba ba matasan shawara a daya daga cikin bayananmu, sai dai a wannan karon, na samu bukatar haka ne daga wani ma’abocin karanta wannan fili.

Tun da farko mai bibiyar mu ne mai suna Malam Hashim Kafinta, Layin NYSC, Kongolam, Jihar Katsina ya aiko da sakon tes kamar haka: “Assalamu alaikum GIZAGO, don Allah ina fatan wata rana wannan fili namu zai yi sharhi game da mutane masu ji-ji-dakai, musamman ma matasa.

“Misali, za ka ga wani matashin saboda ya tashi gidansu akwai kudi ko kuma mulki, bai damu da girmama na gaba da shi ba ko kuma duk wata harka da za ku yi da shi, sai ya wulakanta ka, saboda wai shi a tunaninsa, ya fito daga gidan manya.

“Ko kuma budurwar da za ta dauki karya ta dora wa kanta, alhali wata ma ubanta ba kowa ba ne.”

To, Malam Hashim, ga shi yanzu mun amsa kiranka, kuma za mu dan yi tsokaci game da wadannan bayanai naka, tare da fatan za mu amfana da dan abin da hankalinmu zai tsokanta.

Babbar fa’idar dai ita ce, mu samu tsira daga wannan mawuyaciyar rayuwa ta duniya.

Bari mu dauki al’amari na farko da ka kawo, watau batun irin matasan nan masu dogoro da dukiyar iyayensu ko kuma ganin cewa iyayen nasu na da mulki, wanda ka ce wannan ke sanyawa su dora wa kawunansu girman kai, inda haka kuma ke sanyawa su rika wulakantawa da raina mutane.

A nan, ya kamata irin wadannan matasan su gane cewa, al’amarin rayuwa ya zarce iya tunaninsu, domin kuwa mafi yawan lokaci, ita duniya wata mushkila ce mai rudin rudaddu, mai karkatar da masu karancin tunani, mai jefar da duk wanda ya rungume ta kuma ya ba ta gaskiya.

A nan, ya kamata matasa masu takama da daukakar iyayensu su fahimcicewa, duk mukamin da iyayensu suka samu, walau dukiya ko mulki, ba su same su ne da rana tsaka ba kuma babu wai ba inke, ba gado suka yi ba.

Idan ma gadon ne suka yi, to lallai kam sun ladabtu, sun wahaltu kafin su samu damar rike wannan dukiya ko mulki.

Ke nan su sun ga nasu, to kai kuma fa matashi? Maimakon ka dauki girman kai ka dora wa kanka, kamata ya yi ka kwantar da kanka, ka binciki tarihi, ta yaya iyayen naka suka samu wannan daukaka?

Wace hanya suka bi har suka zama abin da suka zama? Babu shakka ina da yakinin cewa, duk wanda ya zama karkatace a lokacin kuruciyarsa, ba zai samu nasarar daukaka ba.

Don haka, ina da yakinin cewa iyayen nan naku da suka zama daukakakku, sun sha wahala lokacin kuruciyarsu, sun tashi tsaye sun nemi hanyar daukaka a rayuwa, ba su wulakanta mutane ba, kuma ba su sanya girman kai a zukatansu ba.

Abu ne sananne cewa, shi girman kai rawanin tsiya ne, don haka duk matashin da ya sanya wa kansa girman kai, to ga shi can hanyar lalacewa da balbalcewa a rayuwa.

Tarihi yana maimaita kansa ne a dukkan lokaci, domin ban taba ji ko ganin wani mai girman kai ya samu fa’idar rayuwa ba.

Idan haka ne, ya kamata matasa su jefar da wannan mummunan hali na girman kai, su rungumi kyawawan dabi’u domin samun fa’idar rayuwa.

Game da rashin ladabi da kuma wulakanta jama’a kuwa, su ma wadannan wasu munanan halaye ne masu dakile azamar duk wani mutum mai yin su.

Babu shakka inda akuyar gaba ta sha ruwa, nan ma ta baya za ta sha. Don haka, wadannan munanan halaye, duk uwarsu daya kuma ubansu daya da girman kai.

Babu wanda zai samu a yi masa ladabi idan shi bai yi wa wani ba, haka kuma duk wanda ya kasance mai wulakanta jama’a, to shi ma ba zai kai labari ba, domin kuwa shi ma ga shi can a wulakance, yau ko gobe.

Wannan kuwa gaskiya ce, domin mutane na da wata daraja ta musamman, kowa akwai albarkar da Allah Ya zuba masa, ko da kuwa bai mallaki dukiya ko mulki ba.

Don haka, duk wanda ya ce zai wulakanta jama’a, to ba zai wanye lafiya ba.

Ya kamata matasa masu irin wadannan halaye su yi saurin dainawa, kuma su rika mutunta mutane, suna ba wa kowa hakkinsa daidai gwargwado.

Ta haka ne mutum zai wanye da jama’a lafiya, sannan kuma ya wanye da duniya salamun-salamun.

Sai kuma mu koma kan batun Malam Hashim, inda ya yi batun misalin budurwa mai karya da ji-ji-da-kai duk kuwa da cewa ita ba diyar kowa ba ce.

To, duk dai sawa’un da batun matasan farko, domin duk bikin Magaji ne, wanda aka ce bai hana na Magajiya.

Kamar yakin ruwa ne da ya ci sakaina, ta ce mu je zuwa. Babu abin da za mu ce da irin wadannan mata sai dai mu ce kamar ma sun makara a rayuwa, muddin dai suka ce za su dauki wannan turba ta karya da son a sani, alhali ba haka al’amarin yake ba.

Shi dai ramin karya kurarre ne, duk wanda ya ce zai shiga cikinsa, to ba zai rufa masa asiri ba, domin ba da jimawa ba asiri zai tonu, gaskiya ta yi halinta.

A yadda duniya ta sukurkuce, babbar hanya, mikakkiya ita ce abar bi, wacce za ta kai mutum ga mafita, amma ba karya ba da gadara.

Ba zan mace da maudu’in da muka tattauna a kansa ba a kwanakin baya, domin kuwa akwai wani sashi da ya kamata in tsamo daga ciki domin ya sake fa’idantar da matasanmu a nan.

Mun yi bayani ne game da masu shashantar da kansu, su watsar da al’amuran rayuwa, har ma su shantake da cewa, ba za su samu nasarar rayuwa ba.

A cikin bayanin namu, akwai inda muka ce: “Ita nasara fa babu ruwanta da gado, babu ruwanta da cewa babana kaza ne, innata kaza ce, yayana kaza ne.

“Kowa na iya samun nasara, muddin dai ya bi matakan da suka dace. Kana gani, dan talaka sai ya zama sarki, idan dai ya bi matakan zama sarkin.

“Kana gani dan attajiri zai tsiyace, idan bai bi matakan zama attajirin ba. Haka kuma dan malami na iya zama kungurmin jahili, muddin bai bi matakan da zai samu ilimi ba.

“Don haka, rayuwa ’yar tashi a nema ce, kuma neman za a yi shi ne ba da sanyin jiki ba. Za a jajirce, sannan a mai da hankali, idan da rabo sai nasara ta kawo jiki da kanta.”

Shin ko matasanmu za su fahimci wani abu daga wannan bayanin na sama?

Ko za su yi wa kawunansu matashiya, sannan su yi wa kawunan nasu fada domin su canza alkiblar rayuwa?

Domin kuwa al’amarin rayuwa kamar yadda muka ambata can a baya, wata abu ce mai wahalar ganewa, kuma mai wahalar sha’ani.

Amma duk iya wahalarta da muskilancinta, madamar mutum ya bi ta da taka-tsantsan, lallai kam zai samu nasarar wanyewa da ita lafiya, har ma a ce masa san-barka.

Ke nan ya dace mu tunkari duk abin da ya kamata na rayuwa cikin fa’ida da tawali’u da sanin ya kamata.

Shawara ta musamman ga matasanmu maza da mata ita ce, lallai su yi wa kansu kiyamul laili, su fuskanci lamarin gaskiya, su watsar da karya da bagu da rayuwar bogi.

Su mutunta kawunansu sannan kuma su mutunta abokan zamansu, su fitar da girman kai da gadara.

Idan suka yi haka, nasarar rayuwa za ta kasance tasu, ko yau ko gobe. Allah Ya sa mu dace, amin

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara