Girman tumbi ya kubutar da shi daga fadawa a rijiya

Masu aikin ceto a Lardin Henan da ke kasar China sun yaba wa girman tumbin wani dan kasar saboda girman tumbin ya kubutar da shi daga fadawa cikin rijiya. Mutumin wanda jibgege ne ya kubuta daga fadawa cikin rijiyar ce sakamakon girman cikinsa, a daidai lokacin da rijiyar ta afka da shi. Amma kibarsa da […]

Girman tumbi ya kubutar da shi daga fadawa a rijiya

‘Yan kwana-kwana a lokacin da suke ceton tumuli dan China

Masu aikin ceto a Lardin Henan da ke kasar China sun yaba wa girman tumbin wani dan kasar saboda girman tumbin ya kubutar da shi daga fadawa cikin rijiya.

Mutumin wanda jibgege ne ya kubuta daga fadawa cikin rijiyar ce sakamakon girman cikinsa, a daidai lokacin da rijiyar ta afka da shi.

Amma kibarsa da girman tumbinsa suka tukare shi daga zundumawa cikin rijiyar, kamar yadda hukumomi suka bayyana.

Mutumin mai shekara 28 an bayyana sunansa da Mista Liu, kuma ya fada a rijiyar gidansu ce bayan da ya bi ta kan katakon da ake rufe rijiyar da shi, inda rijiyar ta rufta da shi, amma tumbin ya sa ya makale.

Al’amarin ya faru ne a kauyen Fuliudian da ke Lardin Henan, kamar yadda Hukumar Kashe Gobara ta Luoyang ta fitar da rahoton.

Wani bidiyo da Hukumar Kwana-Kwanan ta sanya a kafar sadarwar Intanet a ranar Juma’ar da ta gabata, ya nuna yadda mutumin wanda babu riga a jikinsa ya kalmashe hannu yana jiran masu ceto.

Ya kasance a wannan yanayi tsawon lokaci inda dimbin makwabta suka rika kallon yadda ’yan kwana-kwana su biyar, suka daure kugunsa da igiya mai karfi kuma suka samu nasarar ciccibo shi waje ba tare da tangarda ba.

Hukumar ta bayyana cewa nauyin mutum ya kai laba 500 kimanin kilo 226; amma kafar labarai ta Sun ta ce nauyinsa ya yi kusa laba 300.

Hukumar ta ce ya samu nasarar rayuwa ce saboda kibar da yake da ita wadda ta tokare shi daga fadawa cikin rijiyar a lokacin da katakon da ya rufe rijiyar ya karye da shi.

Liu wanda aka ce ya yi fama da tabin hankali, ya fada rijiyar ne bayan da ya yi tsalle ya dira a kan katakon da aka rufe rijiyar da shi.

A yanzu haka dai iyayensa suna shirye-shiryen rufe rijiyar.

Sojoji Sun Kashe ’Yan Boko Haram 23 A Borno

Fasinjoji sun jikkata yayin da tankar mai ta yi bindiga a Abuja

PDP ta yi watsi da sakamakon zaɓen Edo, za ta garzaya kotu

1.5bn kaɗai aka sanya a asusunmu — Tsohon Kwamishinan Sakkwato