Yadda gishirin lalle ya kashe mutum 22 a Sakkwato

Duk mutanen ’yan gida daya ne, ciki har da wata mata da ’ya’yanta hudu.

Yadda gishirin lalle ya kashe mutum 22 a Sakkwato

Wasu gawarwakin da aka gano bayan hatsarin jirgin ruwa a Jihar Kebbao. (Tshon Hoto: Aliyu M. Hamagam).

Mutum 22 ’yan gida daya sun rasu a lokaci guda sakamakon cin abinci mai guba a kauyen Danzange a Karamar Hukumar Isa ta Jihar Sakkwato.

Kansilan mazabar Bargaja, Mu’azu Kabiru Lugu ya tabbatar mana cewa lamarin da ya jefa mutanen kauyen Danzange a Karamar Hukumar Isa a Jihar Sakkwato cikin damuwa, yi ritsa da matar wani magidanci mai suna Hamidu Makeri da ’ya’yanta hudu.

Ya shaida wa Aminiya cewa lamarin ya faru ne a lokacin da matar Hamidu take dafa abinci, inda ta debo gishirin lalle ta zuba a miyar a matsayin gishiri a a ibtila’in na ranar Asabar da ta gabata.

“Yankinmu yana fama da cutar kwalara, hakan ya sa lokacin da mutanen suka fara amai muka zaci cutar ce ta kama su.

“Amma tunaninmu ya sauya a lokacin da mutum 22 suka rasu su duka a gida daya.

“Da aka bincika aka samu bayanin margayiya ce ta sa gishirin lalle a cikin abincin da ta dafa, wanda ya yi sanadiyyar rasuwarta da ’ya’yanta hudu da matan aure hudu da sauran yara,” inji shi.

Ya gode wa Shugaban Karamar Hukumar Isa, Alhaji Yusuf Dan’ali da Gwamnatin Jihar Sakkwato kan gudunmawar da suka bayar game da rashin da suka yi na mutum 22 a al’ummarsa.

Mijin marigayiyar kuma mahaifin yara hudun, Hamidu Makeri ya ki cewa komai, sai dai ya ce shi dai ya dogara ne ga Allah.

Yadda gwamnati ta yi sulhu da ’yan bindigar Kaduna

‘Da kuɗin yankan farce na je Hajji’

Zambar Intanet: EFCC ta kama ’yan China 4 da wasu 101 a Abuja

Gwamnan Akwa Ibom ya kori duk Kwamishinoninsa