Gishirin rayuwar adon-gari

Bayan Sallama da salama, da fatan malam Dodo uban Dodanni yana cikin koshin uwar jiki da kuzari a jika. Yau Alkalamin rubutun nawa zai karkata ne can jihar da masu yaki da ilimin Bokoko suka addaba, inda har ta kai gishirin zaman duniyar masu adon-gari yana nema ya zama tarihi abin waiwaye. An arce da […]

Gishirin rayuwar adon-gari
Gishirin rayuwar adon-gari

 Mai shelaBayan Sallama da salama, da fatan malam Dodo uban Dodanni yana cikin koshin uwar jiki da kuzari a jika. Yau Alkalamin rubutun nawa zai karkata ne can jihar da masu yaki da ilimin Bokoko suka addaba, inda har ta kai gishirin zaman duniyar masu adon-gari yana nema ya zama tarihi abin waiwaye.
An arce da wasu adon-gari sama da karamin lauje da tsayuwa bisa kafa daya da sili a makarantar kwana ta masu daura dankwali a saman ka, a garin Cibok na jihar barebari. Sabili da haka
ne al’ummar Haurobiya suka yi jugum-jugum suka shiga wani hali. Har ta kai ga iyayen adon gari da masu kishin abin a zukatunsu suka fito muraratan suka yi zanga-zangar nuna alhinin awon gaba da wadannan masu adon-gari a can birnin Harubja, da jihar Tumbin Giwa, da jihar
Bayan Kada da kuma wasu sassa na kasar Haurobiya. Hatta kasashen tsallake sun jajanta wa wadanda suka yi nakudar wadannan masu adon-gari.
Sai dai kuma Arewatawa suna ganin da akwai sakacin shugaba Gudun Kolo da ya bari tsaro ya yi tsami, ana ta ba mutane tsoro maimakon a tsaro da kula da dukiyoyinsu. Anya kuwa shugaba Gudun Kolo damasheren hauron da aka ware don tabbatar da tsaro ba a haure da su wani bangaren ba? E, mana! Watakila tuntuni an yi bandarsu kowa ya kwashi ganimarsa. Ba ma wannan ba! Shin me yasa masu yaki da ilimin bokoko suka fi addabar Arewa da Arewatawa? Ko Arewan ne kawai ake da makarantu da ‘yan Bokoko? Wannan fa tambayar dolen-dole mu dinga sakota jefi-jefi don a irin batu na dokin karfe ana yi mana sakiyar da babu na rijiya ehe. Kuma wai sai a ce za a nada maka na Aura, amma kuma a hana ka gyagijewa da zubda hawaye. Ba haka aka yi wa shugabar mata ta Cibok ba? An garkameta daga kawai an fito an yi zanga-zanga a babban birnin Haurobiya.
To mu dai kam mun shiga malalin gashin tinkiya, domin Barikin Bama ya turo sojojinsu daga Amerika don taimaka wa Haurobiya wajen watsatsake tsamin da tsaro ya yi. Anya kuwa ba damfareren lauje ba ne jikin nadi? Don kuwa munsan halin ‘yan Amerikawa sarai! Kada a jikkatamu a barmu da jinyar jukkunanmu ato!
Saboda haka mu dai babu abin da ya sha mana kai, damuwarmu tsaro ya yi nagarta a Arewa, ta yadda masu adon-gari zasu kwantar da hankalinsu su kwashi tarin gishin zaman duniya a makarantun Bokoko da na Mahammadiya.
Da fatan sauran daliban makarantar malam Dodo sun je Gano domin gano al’amarin da ke wakana.
A huta sumul kalau.
Daga Sulaiman Adamu
shugaban daliban Jihar Bayan Kada
08035931301
08068152670

Martani: Ciwon Cibin-boko
Sallama gare ka Mallam Dodorido.
Da fatan kana cikin koshin lafiya. Na karanta hannun ka mai sandar da kayi a kan garkuwar da aka yi da adon gari, wato ’yan matan garin Cibin-Boko (Chibok) da ke garin Alan-guburo (Borno).
A gaskiya, na jinjina maka, saboda tsari da kuma launin rubutun ka. Don na yi imanin cewa a hausawan ma, daidaiku ne za su iya warware kulle-kullen kalmomin da kayi amfani da su.
Amma ina son in kara jawo hankalin ka game da kalmomin batanci da kake yawaita  yin amfani da su don kaskantar da addinin wani ko kabila. Misali kamar yadda ka kira kungiyar CAN ‘Kungiyar Mabiyar Addini da ke addu’a da giciye’ amma sai ka kira Musulumai a matsayin masu ‘fuskantar alkiblar kadaita Mahilicci da ibada’ wannan ba tsari ba ne.
A gaskiya, kamar yadda na rubuto maka a kwanakin baya. Ba buri na ba ne in ci zarafin addinin wani ko kabilar wani ba. A’a, amma, ina so ka dunga bai wa  kowanne addini ko kabila hakkin su kamar yadda ya dace.
Kuma game da tsokacin da kayi da cewa mu daina dora alhakin kowace irin ta’asa akan masu “HARAMTA BOBO da kwambon BOKOKO (Boko Haram)”. Baka gaya mana irin ta’asa da kake nufi ba. Ko kuma kana tunani cewa ba su da sa hannu a bala’o’in da ke addabar kasar mu ta gado ba?
Na gode, Ubangiji ya sada mu da alkhairin sa.
Dabid Egbele
08039382104

Tsokaci kan Cincirindon Gusun
Assalamu alaikum. Gaisuwa irin ta ma’abota kadaita rabbi Mahalicci cikin bauta ga babban jagora, direban alli da ke watsat-tsake cikin amintacciyar jaridar Haurobiya, wato Malam Dodo, da kuma dukkanin dalibai da ke bin malam sau-da-kafada wajen daukar darasi a farfajiyar makaranta.
Hakika mu dai ba mu da ta fadi illa jin-jina ga daukacin jama’ar  za- mu-fara-shari’a da irin biyar-biyu ta arziki da suka yi wajen tangal-tangal da tarai-rayar cincirindo dalibai da manyan Haurobiya da suka hauro, domin hawar da Dodorido kan dorewa wajen kare harshen Hau-hau, da mutumcin ‘yan Adam. A magaryar tukewa nake fatan kowa ya koma inda ya fito cikin lumana.
A makonnin da suka arce akwai wani mai suna irin na masu kallo yamma wajen neman lada a gicciya, wato Dabid Ebele, inda kwanyar sa ta ba shi sakwar-kwacecce sako, yana fadin wasu kalamai ga Malam, tare da cewa wai malam yana yada kabilanci, tare da kawo sabani cikin Haurobiyawan Haurobiya, Dabid dai ya sani Babban maigidan mu jagoran watsattsake yana watsattsake wajen fadin dokin-karfe ko akan waye, koda yake da ma gaskiya ba ta da zaki a gun mai kinta, don ko a kwanaki da suka arce gwamnan jihar da Fullo-ke-damawa da ya fito ya bayanawa Jatau mai sa’insa. Dokin karfe shi ma ya yi irin wannan.
Mu dai fatan mu Malam Dodo Allah  balluma beii  kugal hairu.
Daga: SABIU UBA YOLA, Shagaban daliban Jihar da Fullo-ke-damawa
07032385544
07055417766.