Giwa mai tauna garwashin wuta ta bayyana a Indiya

A wani faifan bidiyo da aka dauka a Indiya ya nuna yadda wata giwa take fitar da hayaki daga wutar da ta tauna lamarin da ya bai wa kwararru a harkar namun daji a kasashen duniya mamaki.  Masanin kimiyya binay Kumar, wanda dan kungiyar  kare namun daji ne a Indiya shi ne ya dauki hoton […]

Giwa mai tauna garwashin wuta ta bayyana a Indiya

A wani faifan bidiyo da aka dauka a Indiya ya nuna yadda wata giwa take fitar da hayaki daga wutar da ta tauna lamarin da ya bai wa kwararru a harkar namun daji a kasashen duniya mamaki. 

Masanin kimiyya binay Kumar, wanda dan kungiyar  kare namun daji ne a Indiya shi ne ya dauki hoton bidiyon mai tsawon dakika 48 lokacin da suka ziyarci dajin Nagaihole da ke Jihar Karnaka a watan Afrilun shekarar 2016 amma bai fitar da bidiyon ba sai yanzu.

Ya shaida wa BBC cewa sai yanzu ya fitar da bidiyon saboda bai san “abu ne mai muhimanci ba.”

Masana kimiyya sun ce har yanzu ba su san dalilin da ya sa giwar take fitar da hayakin daga bakinta ba.

“Wannan shi ne bidiyo na farko kan wata giwa da ke daji da ta nuna dabi’a irin wannan, kuma wannan ya bai wa masana kimiyya mamaki,” a cewar wata sanarwa da kungiyar kula da namun daji a Indiya ta fitar.

Yadda lamarin ke faruwa

Mista Kumar ya ce shi da ayarinsa sun kai ziyara dajin ne da safe domin su duba kyamarorin da suka saka don daukar hotunan damisa.

Ya kuma hango giwar ce daga wani wuri mai nisan mita 50 kuma ya fara daukar hoto da kyamararsa. 

“Giwar tana tauna gawayin da ke ruruwa wanda yake cikin wutar da aka bari sannan ta fitar da hayaki daga bakinta,” a cewar sanarwar.

“Abin da muka gani a wannan rana ya yi kama da giwar da take shan taba – za ta sa gawayi kusa da bakinta, inda take fitar da bakin hayaki,” inji Mista Kumar. 

Masanin giwaye barun R Goswami, wanda ya yi nazari kan bidiyon, ya yi amanna cewa “watakila giwar tana son ta tauna gawayin ne, yayin da take kokarin daukar wani abu daga kasa, inda take fitar da hayakin da ke tare da abin da ta dauka, tana hadiye sauran.

“Bakin gawayi na da sinadarin Todin, sai dai duk da cewa ba ya da abubuwa masu gina jiki, amma yana jan hankalin namun daji saboda yana yi musu magani,” a cewarsa.