Giwa ta kashe manomi a Uganda

Mataimakin kwamishinan lardin Kudu maso Yammacin Kanungu da ke kasar Uganda Gad Ahimbisibwe Rugaji, ya ce wasu giwaye sun hallaka wani manomi mai shekaru 53 yana tsaka da gadin gonarsa. Sanarwar da mataimakin kwamishinan ya fitar ranar Talata, ya ce giwayen biyu sun hallaka manomin ne mai shekaru 53 mai suna Monday Boniface, a kauyen […]

Giwa ta kashe manomi a Uganda

Mataimakin kwamishinan lardin Kudu maso Yammacin Kanungu da ke kasar Uganda Gad Ahimbisibwe Rugaji, ya ce wasu giwaye sun hallaka wani manomi mai shekaru 53 yana tsaka da gadin gonarsa.

Sanarwar da mataimakin kwamishinan ya fitar ranar Talata, ya ce giwayen biyu sun hallaka manomin ne mai shekaru 53 mai suna Monday Boniface, a kauyen Kememe bayan sun ballo daga Gandun dabbobi na Queen Elizabeth da ke kasar.

Rugaju ya kuma ce giwayen sun fice daga Gandun ba a sani ba, kuma sun lalata gonaki da lamubuna da dama kafin a kamo su a dawo da su.

“Giwayen na cikin gararamba ne suka iske manomin yana gadin gonar dankalinsa da ke kusa da gidansa, kuma take suka hallaka shi.

Rugaji ya ce duk da  mazauna yankin sun dade suna koka wa gwamnati yadda namun dajin ke fitowa daga gandun suna musu barna a gonaki, kada su kuskura su hallaka ko daya daga ciki.

Kwamishinan ya kuma ja hankalinsu wajen tallafa wa gwamnati dawo da dabbobin lafiya idan sun fice ba a sani ba.