Gizagawan Najeriya sun tallafa wa iyalan marigayi Bagizage Abdulmalik danbirni

A karshen makon jia ne ayarin Gizagawa da ta kunshi na jihohin Kano da Jigawa da Kogi da Zamfara ya wakilci Gizagawan Najeriya, wurin kai tallafi ga iyalan margayi Abdulmalik danbirni, a mahaifarsa garin Tattarawa, karamar Hukumar Dawakin Tofa, Jihar Kano. A lokacin da shugaban ayarin, Malam Kabiru Ghali yake gabatar da tallafin, ya ce […]

Gizagawan Najeriya sun tallafa wa iyalan marigayi Bagizage Abdulmalik danbirni
Gizagawan Najeriya sun tallafa wa iyalan marigayi Bagizage Abdulmalik danbirni

A karshen makon jia ne ayarin Gizagawa da ta kunshi na jihohin Kano da Jigawa da Kogi da Zamfara ya wakilci Gizagawan Najeriya, wurin kai tallafi ga iyalan margayi Abdulmalik danbirni, a mahaifarsa garin Tattarawa, karamar Hukumar Dawakin Tofa, Jihar Kano.

A lokacin da shugaban ayarin, Malam Kabiru Ghali yake gabatar da tallafin, ya ce shugaban wannan kungiya na kasa, Malam Muhammad MK Adam Gombe ne ya umarce su da su kawo wannan tallafi na buhun masara biyu da buhun shinkafa daya da katon din taliya daya da kuma Naira dubu 10. An kiyasta adadin agajin gaba daya a kan Naira dubu 50.

A lokacin da ayarin Gizagawan ya shiga wurin mahaifiyar margayin, Malam Kabiru ya shaida mata cewa: “Marigayi danki yana daya daga cikin masu yi wa wannan kungiya ta Gizago hidima na aikin alheri kafin rasuwarsa. Allah Ya jikansa da rahama.”

Ya yi kira ga daukacin Gizagawan Najeriya cewa: “Zan yi amfani da wannan dama in ce mu kara gode wa Allah. Ko a haka muka tsaya, wallahi mun samu nasara. Saboda jin dadin wannan ziyarar kai tallafi, sai da aka dauko Limamin Garin ya yi wa kungiyarmu ta Gizago addu’ar fatan alheri. Allah Ya kara mana juriyar bayar da tallafi duk lokacin da aka nema.

“Daga karshe muna godiya ga Gizagawan da suka tarbe mu a garin su marigayin. Allah Ya saka wa kowa da mafificin alheri, amin.”