Gizgizar Kasa: Adadin wadanda suka mutu a Morocco ya kai 2,500
Girgizar kasar ta kasance mafi muni a tarihin kasar.
Adadin wadanda suka rasa rayukansu a sanadiyar girgizar kasar Maroko, ya kai 2,500, a dai-dai lokacin da kasar ke neman gudunmuwar kasashe don kubutar da ragowar mutanen da ke makale a karkashin buraguzai.
A halin yanzu dai al’amuran kai daukin gaggawa da kuma aikin jin-kai daga kasashen waje game da lamarin na ci gaba da gudana.
- Me ya sa mutane ke luwaɗi da maɗigo?
- ’Yan bindiga sun saki Sakataren Tsare-tsaren APC da suka sace a Kaduna
Tun a ranar Lahadi ne sojojin Spain suka isa kasar Maroko don taimakawa wajen kubutar da wadanda iftila’in ya shafa.
Kasashe da kuma kungiyoyi da dama ne suka bayyana kudirinsu na taimaka wa Maroko kan wannan iftila’in da ya same ta.
Girgizar kasar wacce ta kasance mafi muni a tarihin kasar, ta afku ne a ranar Juma’ar da ta gabata, inda ta hallaka mutane dubu biyu da dari 4 da 97 sannan wasu da dama suka jikkata.
A cewar wasu alkaluma da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar, sun ce sama da mutane dubu dari uku ne girgzar kasar mai karfin maki 6.8 ta shafi, inda ta lalata gidaje da wuraren tarihi tare kuma da sanya dubban mutane kwana a bakin hanya.