Gobara a babbar kasuwar kayan mota a Ibadan
Kasuwar kayan motoci mafi girma a Ibadan Jihar Oyo ta yi gobara.
Kasuwar kayan motoci mafi girma a Ibadan Jihar Oyo, ta yi gobarar a Asabar inda aka yi asarar dukiyoyi masu yawa.
’Yan Kasuwar Araromi da ke Kofar Agodi sun yi ta kururuwar neman dauki yayin da wutar take ci tun kafin wayewar garin Asabar.
- Ya kashe abokinsa saboda musun shekarun haihuwa
- ’Yan bindiga sun kashe Shugabannin Fulani
- Ana bikin daukar gawar Fir’uana a Masar
- Batanci ga Annabi: An kashe matashi an kona gawarsa a Bauchi
Wasu kayan fashewa da suka rika yin bindiga a yayin da wutar ke ci sun sa abin ya kara ta’azzara musamman a bangaren masu sayar da tayoyi, inda wutar ta fi barna.
Bayan tashin gobarar a safiyar Asabar, wasunsu sun yi ta kokarin kiran hukumar kashe gobarar ta Jihar Oyo, saura kuma suka bazama kokarin kashe wutar.
Majiyarmu ta ce jami’an kashe gobarar sun fuskanci matsala kafin su samu karasawa inda wutar take ci, saboda yadda wasu kananan kantuna suka tare hanyar.
’Yan kasuwar sun ce kayan da aka fi yin asara sun hada da kayan motoci da tayoyi, amma ba a kai ga tantance musabbabin tashin gobarar ko kuma asarar rai ba.