Gobara: Abba ya ba ’yan kasuwar Kantin Kwari gudunmawar N100m

Abba ya kuma bayyana cewar manufar ba da wannan gudunmawar ita ce rage wa ‘yan kasuwar raɗaɗin iftila’in da ya ritsa da su.

Gobara: Abba ya ba ’yan kasuwar Kantin Kwari gudunmawar N100m

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa gudunmawar Naira miliyan 100 ga waɗanda iftila’in gobara ya afkawa a shahararriyar kasuwar tufafin nan ta Kantin Kwari.

Gwamnan wanda ya jagoranci tawagar ƙusoshin gwamnati ya miƙa gudunmawar ne yayin ziyarar da ya kai kasuwar, inda ya bayyana jajensa ga waɗanda lamarin ya shafa.

Abba ya kuma bayyana cewar manufar ba da wannan gudunmawar ita ce rage wa ‘yan kasuwar raɗaɗin iftila’in da ya ritsa da su.

Ya ƙara da cewa, “duk da cewa kuɗaɗen ba za su iya mayar da asarar da aka yi ba, amma manufar hakan ita ce taimaka wa waɗanda lamarin ya shafa rage raɗaɗi.”

Ana iya tuna cewa, Aminiya ta ruwaito cewa ɗaukin gaggawa da ’yan kwana-kwana suka kai ya taimaka wajen shawo kan gobarar da ta lalata shaguna 29.

Shugaban Hukuma Kasuwar Kantin Kwari, Alhaji Sa’ad Hamisu Dogon Nama, ya bayyana godiya ga ɗaukin da aka kawo musu.

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya

Kano: Kwamishinan da Abba ya tsige ya koma Jam’iyyarAPC