Gobara: Gwamnatin Yobe ta tallafa wa ’yan kasuwar Damaturu da Gashua
SEMA ta ba su tallafin buhun shinkafa guda 200 domin rage musu raɗaɗi.
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bai wa ’yan kasuwar da gobara ta shafa a Damaturu da Gashua tallafi, domin rage musu raɗaɗin asarar da suka yi.
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) ce, ta raba musu buhun shinkafa guda 200.
- Mun yi bankwana da ECOWAS babu batun dawowa – Nijar, Mali da Burkina Faso
- Zamana a gidan yari jarabawa ce daga Allah – Farouk Lawan
A yayin rabon tallafin a Gashua, shugaban Ƙaramar Hukumar, Ibrahim Babagana Yurema, ya gode wa gwamnatin Jihar bisa ɗaukar matakin tallafin.
Ya kuma tabbatar da cewa za su raba kayan cikin gaskiya da adalci don taimaka wa waɗanda suka rasa dukiyoyinsu.
A Damaturu kuwa, shugaban ƙungiyar ‘yan kasuwar Jihar Yobe, Alhaji Mukthar Kime, ya karɓi tallafin a madadin waɗanda gobarar ta shafa.
Ya yi alƙawarin tabbatar da cewa duk kayan tallafin za su isa hannun masu buƙata ba tare da nuna bambanci ba.
Babban Sakataren SEMA, Dokta Mohammed Goje, ya jaddada buƙatar yin haɗin gwiwa wajen kauce wa ɓarkewar gobara, musamman a lokacin hunturu.
Gwamnatin Jihar ta kuma gode wa dukkanin waɗanda suka bayar da gudunmawa wajen ganin wannan tallafi ya samu nasara.