Gobara: Mutum 100 sun rasu, an ceto 417 a Kano a 2023
Kakakin hukumar ya ce sun samu kiran agaji guda 659 a 2023.
Mutane akalla 417 ne suka tsallake rijiya da baya daga gobarar da aka samu a Jihar Kano shekarar 2023.
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ta sanar cewa wasu mutum 100 sun rasa rayukansu, yayin da aka yi asarar kadarorin sama da Naira miliyan 45 a fadin jihar a shekarar.
- DAGA LARABA: Ina Aka Kwana A Binciken Harin Tudun Biri?
- An sako shugaban karamar kukumar Akwanga da aka sace bayan biyan N10m
Kakakin hukumar, Saminu Abdullahi ne, ya shaida wa da kamfanin dillacin labaran Najeriya (NAN), cewa sun samu kiran neman agaji 659 a shekarar.
A cewarsa, jami’ana sun kuma yin asarar da ce daukiyar biliyan N1.2 daga gobara a wurare daban-daban a shekarar.
Abdullahi ya ce sun amsa kiran agaji na gaskiya 299 da kuma na karya 95 daga mazauna jihar da kuma kiran agaji 184 a kan hatsarin titi.
Kakakin ya danganta tashin gobarar da rashin kula da gas din girki, amfani da na’urorin lantarki da adana man fetur a gidaje da sauransu.
Ya shawarci al’ummar jihar da su yi taka-tsan-tsan yayin da suke sarrafa abubuwan da ka iya haifar da gobara.
“Masu jin dumi musamman a lokacin sanyi a kasuwa ko bakin titi, ya kamata su kashe wutar da isasshen ruwa don guje wa yanayin da ba a shirya masa ba.
“Ya kamata iyaye su kasance masu sanya ido kan ’ya’yansu, musamman wadanda ke zuwa rafi wanka don guje wa nutsewa ko wani abu daban,” in ji shi.