Gobara: NEMA ta raba kayan abinci a Zamfara da Sakkwato 

Hukumar ta ce ra raba kayan ne domin rage wa waɗanda lamarin ya shafa raɗaɗi.

Gobara: NEMA ta raba kayan abinci a Zamfara da Sakkwato 

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), ta raba kayan abinci da dama ga waɗanda gobarar Gusau da Sakkwato ta shafa.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban NEMA na ayyuka a Sakkwato, Mista Aliyu Shehu-Kafindangi, ya fitar a Gusau ranar Asabar.

“NEMA ta raba kayan abinci ga waɗanda gobarar Gusau da Kasuwar Sakkwato ta shafa a farkon wannan shekarar.

“Kayan abincin tallafin gwamnatin tarayya ne ga waɗanda abin ya shafa don rage musu raɗaɗi.

“An gudanar da rabon kayayyakin a lokaci guda a jihohin Zamfara da Sakkwato.

“NEMA ta gudanar da rabon kayayyakin a Sakkwato da Gusau domin tabbatar da cewa waɗanda abin ya shafa sun samu agaji,” in ji Shehu-Kafindangi.

Ya bayyana cewar shi ne ya jagoranci rabon rabon a Zamfara a madadin Darakta Janar, Misis Zubaida Umar.

Shehu-Kafndangi, ya ce “Mista Aminu Ambursa ne, ya jagoranci rabon kayayyakin a Sakkwato,” in ji

Shehu-Kafndangi.

Ya ce rabon kayan abincin da aka yi a jihohin Zamfara da Sakkwato, an yi su ne ta hanyar haɗin gwiwa da Ma’aikatar Bayar da Agaji ta Zamfara da Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Sakkwato.

Matashi ya kashe mahaifinsa kan N5,000 a Delta

Muhimman batutuwa da Biden ya taɓo a jawabin yi wa Amurkawa bankwana

IPMAN ta musanta batun ƙara farashin man fetur

Gwamnatin Tinubu ta yi wa Sarki Sanusi raddi