Gobara ta ƙone gidaje, amfanin gona da dabbobi a Borno 

Gobarar ta ƙone amfanin gona, gidaje da kuma dabobbi na miliyoyin Naira.

Gobara ta ƙone gidaje, amfanin gona da dabbobi a Borno 

Wata gobara ta tashi a ƙauyen Bukar da ke Ƙaramar Hukumar Konduga a Jihar Borno, ta yi ɓarna mai tarin yawa.

Gobarar ta lalata gidaje, amfanin gona, da dabbobi na miliyoyin Naira, amma babu wanda ya rasa ransa.

Wani mazaunin ƙauyen ya ce gobarar ta fara ne daga wutar girki a wani gida, sai iska mai ƙarfi ta bazata zuwa wasu gidaje, lamarin da ya sa mutane suka kasa shawo kanta.

Bayan kamawar wutar, sojojin Najeriya da ke yankin sun garzaya domin kai ɗauki.

Sun taimaka wajen kashe wutar tare da ceton tsofaffi da yara.

Kazalika, gobarar ta cinye wani ɓangare na kasuwar ƙauyen, inda ta ƙone shaguna da rumfunan abinci.

Mazauna ƙauyen sun ce yanayin iskar da ake yi a lokacin ya ƙara ta’azzara gobarar, hakan ya sa aka wahala wajen kashe ta.

Duk da hatsarin da ke tattare da wutar, sojoji sun taimaka wajen daƙile gobarar, wanda ya hana ta bazuwa zuwa wasu wurare, ciki har da makarantar ƙauyen.

Shugabannin yankin sun nuna godiyarsu ga sojojin da suka kawo musu ɗauki cikin gaggawa.

“Ba don taimakon Allah da na sojoji ba, gobarar na iya haddasa asarar rayuka,” in ji wani mazaunin ƙauyen, Bukar Usman.

A halin yanzu, Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Borno (SEMA), ta tura tawaga domin tantance asaea tare da raba kayan agaji ga waɗanda gobarar ta shafa.