Gobara ta ƙone motoci da shaguna a wajen sayar da gas a Neja
Wutar ta ɗauki lokaci tana ci kafin zuwan jami’an hukumar kashe gobara.
![Gobara ta ƙone motoci da shaguna a wajen sayar da gas a Neja Gobara ta ƙone motoci da shaguna a wajen sayar da gas a Neja](https://aminiya.ng/wp-content/uploads/2025/02/img_20250209_082705.jpg)
Wata gobara da ta tashi a wajen sayar da gas a Sabon Wuse da ke Ƙaramar Hukumar Tafa a Jihar Neja, ta yi sanadin ƙonewar motoci da shaguna da kuma kayan abinci.
Lamarin ya faru ne a daren ranar Asabar lokacin da wata tanka ke sauke gas a wajen sayar da gas.
- Gwamnatin Kano ta dakatar da wani fim mai suna Zarmalulu
- Me ya sa ake musayar yawu tsakanin APC da PDP?
Wutar ta ɗauki sa’o’i tana ci kafin isowar jami’an kashe gobara.
Wani mazaunin garin, Abdul Sabon-Wusa, ya ce bindigar ta girgiza yankin, inda mutane suka firgita suka fito daga gidajensu domin neman mafaka.
Wutar ta kuma bazu zuwa wani gidan mai, inda ta ƙone shaguna da motoci da aka ajiye.
“Muna godiya ga Allah ba a rasa rai ba, kuma ba a samu wanda ya jikkata ba.
“Idan hakan ta faru da rana lokacin da mutane ke kasuwancinsu, da wani babban iftila’in ne zai faru,” in ji shi.
Ya ce hayaƙin gobarar ya tashi sama sosai har ana iya ganinsa daga sassa daban-daban na garin, wanda ke nuna yadda wutar ta yi ƙamari.