Gobara ta ƙone shaguna 17 a tsohuwar kasuwar Gombe

Mutanenmu da dama sun saro kaya a kwanan nan, amma yanzu duk sun ƙone.

Gobara ta ƙone shaguna 17 a tsohuwar kasuwar Gombe

Wata mummunar gobara ta ƙone shaguna sama da 17 a ɓangaren ’yan teloli da masu hada-hadar kayan abinci a tsohuwar kasuwar garin Gombe.

Gobarar, wadda ta fara da misalin ƙarfe 2:00 na dare, ta jefa ’yan kasuwa cikin jimamin asarar dukiya mai tarin yawa da aka kiyasta ta kai miliyoyin naira.

Wasu da lamarin ya faru a kan idonsu, sun bayyana cewa gobarar ta bazu cikin sauri, inda ta riƙa laƙume kaya da kadarori kafin ’yan kwana-kwana su iso wurin.

Ko da yake ba a tabbatar da musabbabin tashin gobarar ba, amma wasu ’yan kasuwar na zargin cewa matsalar wutar lantarki ce ta haddasa ta.

Wani daga cikin ’yan kasuwar da lamarin ya shafa, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana bakin cikinsa da cewa, “Mun rasa komai.

“Mutanenmu da dama sun saro kaya a kwanan nan, amma yanzu duk sun ƙone. Wannan babban kalubale ne a gare mu.”

Wakilinmu ya ruwaito cewa jami’an hukumar kashe gobara ta Jihar Gombe tare da gudunmawar wasu mazauna ne suka taimaka wajen hana gobarar bazuwa zuwa wasu sassan kasuwar.

Sai dai, kafin a kashe gobarar gaba ɗaya, tuni ta riga ta yi mummunar ɓarna.

Har yanzu mahukunta ba su fitar da wata sanarwa game da lamarin ba, sai dai shugabannin ’yan kasuwa suna kira ga gwamnati da ta taimaka wa ’yan kasuwar da abin ya shafa.

Sun kuma yi kira da a ɗauki tsauraran matakan daƙile gobara don hana faruwar irin wannan lamari a nan gaba.

Wannan gobarar ta shiga jerin gobarar da suka auku a kasuwannin Gombe a cikin ’yan shekarun nan, lamarin da ya jaddada muhimmancin samar da ingantattun matakan daƙile aukuwarta a wuraren kasuwanci.