Gobara ta ƙone shaguna 30 da dukiya a kasuwar Nasarawa

Wata gobara da ta tashi a daren ranar Alhamis ta ƙone aƙalla shaguna 30 a wata kasuwa ds ke Jihar Nasarawa, inda ta janyo asarar miliyoyin Naira. 

Gobara ta ƙone shaguna 30 da dukiya a kasuwar Nasarawa

Wata gobara da ta tashi a daren ranar Alhamis ta ƙone aƙalla shaguna 30 a wata kasuwa ds ke Jihar Nasarawa, inda ta janyo asarar miliyoyin Naira.

Gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 9:30 na dare, har zuwa safiyar ranar Juma’a, yayin da masu kashe gobara suka sha wahala wajen shawo kanta saboda tarkace da suka yi yawa a kasuwar da kuma zafin wutar.

Wani mai shago, Musa Abdullahi da gobarar ta ƙone masa shago, ya bayyana halin da ya shiga.

“Kusan kashi 70 na shagunan kasuwar nan sun ƙone. Sabbin kekunan ɗinki guda 40 da aka kawo da safiyar ranar Alhamis duk sun ƙone, tare da shaguna uku na mahaifina.

“Sauran shagunan da suka ƙone sun haɗa da masu sayar da takalma da kaya.”

Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Nasarawa, Builder Ombogus-Joshua, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce: “Mun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 9:30 na dare kuma nan da nan muka aike tawagarmu zuwa wajen.

“Duk da cewa shaguna 30 sun ƙone, ba a tabbatar da adadin waɗanda suka ƙone ba tukuna. Ana ci gaba da bincike.”