Gobara ta ƙone shaguna 50 a kasuwar kara a Sakkwato
Wutar ta tashi ne cikin dare lokacin da kowa ba ya nan.
Gobara ta tashi a kasuwar Kara da ke Sakkwato a daren ranar Juma’a, inda ta lakume shaguna kusan 50 da dukiyar mai tarin yawa.
Sai dai ba a samu asarar rayuka ba.
Gobara ta fara ne a ɓanagaren markaɗe, inda ta ƙone shaguna da injin niƙa da dama.
Shugaban ƙungiyar masu sana’ar, Yakubu Bello, ya ce gobarar ta faru ne a lokacin da kowa ya tashi daga aiki.
Kuma ya ce har kawo yanzu ba a gano musababbin tashin wutar ba, domin babu wutar lantarki a lokacin.
“Mun yi babbar asara. Aƙalla shaguna 45 zuwa 50 ne suka ƙone, sannan injin niƙa manya kusan 100 sun salwanta, gaba ɗaya inji 132 muka rasa,” in ji Yakubu.
Ya yi kira ga gwamnati da ta taimaka musu, saboda matasa kusan 500 ne suka dogaro da wannan sana’ar.
Wani mai sana’ar niƙa, Aminu Mainika Gandu, ya ce: “Gobara ta fara ne misalin ƙarfe 11:30 na dare, an kira ni a waya.
“Zuwa lokacin da na isa wajen, komai ya ƙone. Sai dai muna godiya ga ma’aikatan kashe gobara da suka hana wutar bazuwa zuwa sauran sassan kasuwar.”
Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, ya jajanta wa waɗanda suka yi asara, inda ya yi addu’ar Allah Ya mayar musu da alheri.
A nasa ɓangaren, Mataimakin Gwamnan Sakkwato, Alhaji Idris Muhammad Gobir, ya ce gwamnati za ta kafa kwamitin bincike don gano musababbin tashin gobarar da kuma hanyoyin kaucewa irin wannan a gaba.
Ya tabbatar da cewa gwamnati za ta taimaka wa waɗanda gobarar ta shafa.