Gobara ta ƙone uwa da ɗanta ƙurmus a Abuja

Gobarar ta ƙone matar da ɗanta ƙurmus har lahira.

Gobara ta ƙone uwa da ɗanta ƙurmus a Abuja

Wani gini yana ci da wuta

Wata gobara da ta tashi cikin dare, ta ƙone wata mata mai suna Jumai Sunday, mai shekara 24 tare da ɗanta, Nasir Rabiu, mai shekara shida.

Gobarar ta tashi ne a wani gida da ke kasuwar kayan ɗaki ta Kugbo da ke Ƙaramar Hukumar AMAC, a Abuja.

Marigayiyar, wadda ‘yar asalin Ƙaramar Hukumar Eggon ta Jihar Nasarawa ce, tana tare da ɗanta ɗaya tilo lokacin da gobarar ta tashi a ranar Laraba.

Shaidu, sun bayyana cewa gobarar ta ƙone matar da ɗan nata ƙurmus, duk da ƙoƙarin jami’an kashe gobara na shawo kan lamarin.

Maƙwabta da masu zuwa jaje ne suka gano gawarwakinsu a lokacin da suka je gyara kadarorinsu da gobarar ta lalata.

Jami’in ’yan sanda mai kula da yankin Karu, Lakur Langyi, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce jami’an tsaro sun samu kiran gaggawa ciki dare daga yankin, inda inda suka je suka gano gawarwakin matar da ɗanta.

Ya kuma bayyana cewa har yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar ba.

Amma, ya ce sun fara gudanar da bincike don gano musababbin tashin gobarar.