Gobara ta ci jarirai 12 a Iraki

Akalla jarirai bakwaini 12 ne suka mutu a wani asibiti da ke birnin Bagadaza na kasar Iraki sanadiyyar tashin wata gobara a shekaranjiya Laraba.Wata sanarwa da ma’aikatar lafiyar kasar ta fitar ta ce gobarar ta tashi ne da tsakar daren ranar Talata, a bangaren masu haihuwa na asibitin koyarwa na Yarmouk da ke yammacin birnin.Sanarwar […]

Gobara ta ci jarirai 12 a Iraki
Gobara ta ci jarirai 12 a Iraki

Akalla jarirai bakwaini 12 ne suka mutu a wani asibiti da ke birnin Bagadaza na kasar Iraki sanadiyyar tashin wata gobara a shekaranjiya Laraba.
Wata sanarwa da ma’aikatar lafiyar kasar ta fitar ta ce gobarar ta tashi ne da tsakar daren ranar Talata, a bangaren masu haihuwa na asibitin koyarwa na Yarmouk da ke yammacin birnin.
Sanarwar ta kara da cewa an samu ceto wasu jarirai bakwai da mata 29 kuma an maida su wasu asibitocin, kamar yadda BBC ta bayyana.
Wasu majiyoyi sun ce an bai wa jarirai 19 maganin kuna da suka samu da kuma shakar hayakin da suka yi.
Ma’aikatar lafiyar ta ce watakila gobarar ta tashi ne sakamakon matasalar da aka samu ta wutar lantarki.
Wani mai ba wa Ministan Lafiyar kasar Shawara Dokta Amir al-Mukhtar ya ce jirajirai 20 ne suke dakin jinyan a lokacin da wutar ta fara.
Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ce wani jami’i daga ma’aikatar lafiyar kasar, Jassem Lateef al-Hijami, ya ce “asibitin ya tsufa matuka don haka ba shi kayayyakin kashe gobara”.
Wata mata mai suna, Shaimaa Hassan, mai shekara 36 da haihuwa, wadda ta rasa jinjirinta a gobarar ta isa harabar asibitin a safiyar shekaranjiya Laraba. Ta ce “gobarar ta ci jinjirina wanda na Haifa kwana biyu da suka wuce”.
“Na kwashe shekaru ina neman haihuwa, sai bayan da na samu haka ne kuma ga shin a rasa abin da haifa,” inji ta.
Babu cikakken bayani kan batun, sai dai ana samun rahotanni na karuwar gobara sanadiyyar matsalar wutar lantarki a ma’aikatu da manyan kantuna a kasar a ‘yan shekarun nan.