Gobara ta ci ofishin ’yan sanda a Kano

Gobara ta tashi a Babban Ofishin ’yan sanda da ke unguwar Dakata a Jihar Kano.

Gobara ta ci ofishin ’yan sanda a Kano

’Yan sanda a caji ofi din Obosi bayan harin. (Hoto: Titus Eleweke, Awka)

Gobara ta tashi a Babban Ofishin ’yan sanda da ke unguwar Dakata a Karamar Hukumar Nassarawa a Jihar Kano.

Kwamishinan yan sandan jihar, Usaini Gumel, ya ce gobarar ta safiyar Litinin, “ta kone wani bangare gaba daya a babban ofishin ’yan sandan da ta tashi.

“Amma duk haka, babu abin da ya sami makaman da ke ofishin.”

Kwamishinan ’yan sandan ya ce tashin gobarar ke da wuya, jami’an hukumar kashe gobara ta jihar suka zo suka kashe ta, kuma ana bincike don gano musabbabin tashinta.

“An killace wurin domin hana masu kallo da miyagu shiga, kuma DPO na yankin yana kan tantance wasu takardun da abin ya shafa,” inji shi.

An ƙaddamar wa ’yan kasuwa sabon tsarin biyan haraji a Gombe

Majalisa na son ƙirƙiro sabbin jihohi 31 a Najeriya

Malamai sun fara yajin aiki a Ebonyi

Mutuwar Almajirai: Tinubu ya buƙaci a samar da matakan kare ɗalibai