Gobara ta ci shaguna 40 a kasuwar Kuros Ribas
Akalla shaguna 40 ne gobara ta ci da kuma dukiyar miliyoyin nairori a kasuwar Ikom da ke Jihar Kuros Ribas. Gobarar ta fara ne da misalin karfe 2:00 na daren ranar Talata kuma an danganta tashinta ne da matsalar wutar lantarki. Rahotanni sun ce an tuntubi ‘yan kwana-kwana garin Ikom a kan lokaci, amma ba […]

Akalla shaguna 40 ne gobara ta ci da kuma dukiyar miliyoyin nairori a kasuwar Ikom da ke Jihar Kuros Ribas.
Gobarar ta fara ne da misalin karfe 2:00 na daren ranar Talata kuma an danganta tashinta ne da matsalar wutar lantarki.
Rahotanni sun ce an tuntubi ‘yan kwana-kwana garin Ikom a kan lokaci, amma ba su karasa wurin ba saboda karancin kayan aiki kamar yadda suka bayyana.
Zuwa lokacin hada wannnan rahoton ba a iya tabbatar da ko an samu asarar rai ba.