Gobara ta ci shaguna sama da 100 a kasuwar Singa
A safiyar jiya Alhamis ne wata gobara ta tashi a Kasuwar Singa da ke Kano inda ta ci dukiya ta biliyoyin Naira.Aminiya ta ziyarci kasuwar inda ta ga yadda gobarar ta kone shaguna sama da 100 a rukunin gidan Abdurrashid Hamza Maiturare.Rahotanni sun bayyana cewa gobarar ta tashi ne da misalin karfe 3:00 na dare, […]

A safiyar jiya Alhamis ne wata gobara ta tashi a Kasuwar Singa da ke Kano inda ta ci dukiya ta biliyoyin Naira.
Aminiya ta ziyarci kasuwar inda ta ga yadda gobarar ta kone shaguna sama da 100 a rukunin gidan Abdurrashid Hamza Maiturare.
Rahotanni sun bayyana cewa gobarar ta tashi ne da misalin karfe 3:00 na dare, ba ta kuma tsagaita ba har zuwa karfe 2:00 na rana.
Haka kuma ana zaton gobarar ta tashi ne daga wurin wani mai shayi da ke gefen ginin shagunan da gobarar ta kama, inda kuma wata tukunyar gas din da wasu ke sana’ar gugguru da shi ta fashe wanda ya yi sanadiyyar fantsamar wutar cikin kasuwar .
Abba Dogo yana daya daga cikin wadanda gobarar ta cinye wa shago, ya bayyana wa Aminiya cewa gobarar ta cinye masa shagonsa tas, domin babu abin da ya dauka a shagon nasa.
Sai dai Abba Dogo ya dora alhakin karuwar gobarar a kan gwmanati, inda ya ce,”lokacin da muka iso kasuwa shaguna da yawa ba su kama da wutar ba, amma saboda rashin kayan aiki na Hukumar kashe gobara muna ji muna gani wutar ta shiga shagunanmu suka cinye kurmus babu abin da za mu iya yi akai. Yawanci kamfanonin masu zaman kansu ne suka taimaka wajen kashe gobarar. Na tabbata da a ce akwai isassun kayan aiki, to da asarar ba ta kai haka ba”. Inji shi.
Shi ma Malam Sabi’u Muhamamd ya bayyana cewa ya yi asarar sama da Naira miliyan 6 a gobarar. “Ni kaina na yi asarar dukiya da ta kai Naira miliyan shida. Akwai kuma mutanen da suka yi asarar sosai. Kin san gidan babba ne, shaguna ne sama da kasa. Sannan ga masu faleti da tebura. Akalla an yi asarar da ta doshi Naira biliyan biyar ko ma samada haka.”
Malam Sabi’u sai ya yi kira ga gwamnati da ta kawo wa ‘yan kasuwar nasu dauki, “Muna so gwmnati ta tallafa wa wadanda wananngobara ta rutsa da su. Dama dai ana cikin wani yanayi na rashin ciniki sai kuma ga wata jarrabawa daga Allah. Mun san cewa gwamnati ba za ta iya mayar mana da abin da muka rasa ba, amma dai idan aka tallafa mana za mu ji dadi,” Inji shi.
Alhaji Umar Hussaini Gabari shi ne Shugaban Hadaddiyar kungiyar ‘Yan kasuwa ta Amata reshen Kasuwar Singa, ya bayyana cewa,r “Wanann gobara da ta tashi ta ci shaguna sama da 100. Muna kira ga gwamnati da ta kawo wa wadannan mutane tallafi don su samu dan abin da za su su yi jari da shi. Mutane da yawa sun yi asara sosai, domin babu abin da suka iya dauka a shagunansu.”
Shi kuwa Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano Malam Balarabe Habu Kabara bayyanawa ya yi cewa, bincikensu ya gano cewa gobarar ta tashi ne daga wurin mai shayi da ke kasuwar. “Bayan an sanar da mu mun isa wurin a kan lokaci inda muka yi kokarin kashe wutar, a nan ne ma har jami’anmu su uku suka samu raunika.
A cewar Shugaban Hukumar Kashe Gobarar, rashin isasshiyar hanya a cikn kasuwar ne abin da ya kawo tarnaki wajen aikin dasuka yi na kashe wutar.