Gobara ta ci uwa da danta a Katsina
Wata gobara da ta tashi a gidan wani mai suna Alhaji Muntari Allah Wahid ta yi sanadiyar rasuwar matarsa da dansa yayin da ’yarsa mai kimanin wata biyu ta tsira. Alhaji Muntari ya shaida wa Aminiya cewa, wutar ta tashi ne da misalin karfe 4:20 na asuba a shekaranjiya Laraba a gidansa da ke Unguwar […]
Wata gobara da ta tashi a gidan wani mai suna Alhaji Muntari Allah Wahid ta yi sanadiyar rasuwar matarsa da dansa yayin da ’yarsa mai kimanin wata biyu ta tsira.
Alhaji Muntari ya shaida wa Aminiya cewa, wutar ta tashi ne da misalin karfe 4:20 na asuba a shekaranjiya Laraba a gidansa da ke Unguwar ’Yarkasuwa da ke cikin garin Katsina.
“Da misalin karfe 5:40 hayakin wutar ya tayar da ni daga barci, kuma ina farkawa na tayar matata Jamila da muke kwance a uwar daka, yayin da wutar ke ci a falo. Babu wutar lantarki a lokacin, kuma ganin yadda wutar ke tashi, sai na yi yunkurin shiga ta cikin wutar domin zagayawa bayan dakin don in cire karfen tagar dakin ta yadda zan samu sukunin fitar da Jamila da jaririyar da take goyo mai suna Zainab tare da Umar wanda a lokacin da nake kokarin fita daga cikin wutar ban ga ya motsa ba,” inji shi.
Ya ce: “Lokacin Jamila tana ce mini in na shiga cikin wutar zan kone, na ce wannan konewar ta fi sauki. Sai ta tayar da babban dana Abba wanda da shi muka zagaya baya muna kokarin cire karfen da hannu. Ashe lokacin da muke wannan kokari zafin wutar da ke kara haukata da hayaki sun galabaitar da Jamila. Allah cikin ikonsa, lokacin da muka cire karfen tagar sai na ga ashe ta ajiye Zainab bisa bangon tagar dakin daga ciki. Muna cirewa Zainab na sulalowa ni da Abba muka tarbe ta. Lokacin da nake kiran ta (Jamila) tuni rai ya yi halinsa.”
Alhaji Muntari wanda ya dora wannan al’amari ga Allah ya ce, ba su san musabbabin wutar ba ballantana hakikanin lokacin da ta fara ci a cikin falon ba.
Marigayiya Jamila mai shekara 38 ta rasu ta bar mijinta Muntari Allah Wahid da ’ya’ya shida, yayin da Umar ya rasu yana da shekara 4.
An yi jana’izarsu kamar yadda addinin Musulunci ya shimfida.