Gobara ta cinye ofishin Kungiyar NLC a Sakkwato
Gobarar, wadda ta fara ne misalin ƙarfe 3:00 na asuba, ta cinye ɗaukacin ginin, ba tare da an iya ceto komai ba.
Wata gobara da ta tashi da asuba ta cinye ofishin Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) reshen Jihar Sakkwato, inda ta lalata dukkan kayayyaki da muhimman takardu na tsawon fiye da shekaru 30.
Gobarar, wadda ta fara ne misalin ƙarfe 3:00 na asuba, ta cinye ɗaukacin ginin, ba tare da an iya ceto komai ba.
Sakataren Ƙungiyar NLC na jihar, Hamisu Hussaini Hamisu, ya bayyana cewa ana zargin gobarar ta samo asali ne daga matsalar wutar lantarki.
Ya ce wutar ta bazu cikin sauri, inda ta ƙone kwamfutoci da firintoci da irinji, talabijin da kujeru da sauran kayayyakin ofis.
Hamisu ya ƙara da cewa dukkan muhimman bayanai da suka shafi fiye da shekaru 30 sun salwanta, lamarin da ya kira babban koma baya ga ƙungiyar.
Rahotanni sun ce mai gadi da ke bakin aiki ya yi ƙoƙarin kashe gobarar amma ya kasa saboda yadda ta bazu cikin gaggawa.
An ce ma’aikatan kashe gobara sun iso wurin bayan kusan awa guda, inda daga bisani suka samu nasarar daƙile wutar.
Sai dai an bayyana asarar a matsayin ta ɗungurungum, domin babu wani abu da aka iya fitarwa daga cikin ginin.
Lamarin ya girgiza ƙungiyar kwadago a jihar, inda yanzu hankula suka karkata ga yadda za a farfaɗo da ayyuka da kuma sake gina ofishin.