Gobara ta cinye shaguna 31 a kasuwar Gumi Kaduna
A yau Laraba ne tashin gobara ya yi sanadiyyar cinye shaguna 31 da kayan abinci da ya kai na miliyoyin Naira a kasuwar Shaikh Gumi da ke Bakin Dogo jihar Kaduna. Rahotanni na bayyana cewa, gobarar ta tashi ne da misalin karfe 2:00 na dare, yayin da ‘yan kasuwan kowa na gidansa sai dai kawai […]
A yau Laraba ne tashin gobara ya yi sanadiyyar cinye shaguna 31 da kayan abinci da ya kai na miliyoyin Naira a kasuwar Shaikh Gumi da ke Bakin Dogo jihar Kaduna.
Rahotanni na bayyana cewa, gobarar ta tashi ne da misalin karfe 2:00 na dare, yayin da ‘yan kasuwan kowa na gidansa sai dai kawai masu gadin kasuwar.
Ba a bayyana sanadiyyar tashin gobarar ba, amma wasu masu tireda sun dora alhakin tashin gobarar ga wutar lantarki.
Wadanda gobarar tafi wa asara su ne masu sayar da rogo da garin masara da ke hanyar Birnin Kudu yankin kasuwar Bakin Dogo.