Gobara ta cinye shaguna 77 a kasuwar Kano

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta sanar da cewa, gobarar da aka yi a Kasuwar Kurmi (‘Yan Gumama) a jihar ta cinye shaguna 77. Kakakin hukumar Alhaji Saidu Mohammed ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai NAN a Kano cewa, shaguna 70 daga cikin shagunan sun kone kurmus. Hukumar ta samu sanarwar barkewar gobarar ne […]

Gobara ta cinye shaguna 77 a kasuwar Kano

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta sanar da cewa, gobarar da aka yi a Kasuwar Kurmi (‘Yan Gumama) a jihar ta cinye shaguna 77.

Kakakin hukumar Alhaji Saidu Mohammed ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai NAN a Kano cewa, shaguna 70 daga cikin shagunan sun kone kurmus.

Hukumar ta samu sanarwar barkewar gobarar ne lokacin da wani Aliyu Ibrahim ya kira ta wayar  tarho da misalin karfe 07:35 na safe ranar Lahadi, don sanar da gobarar.