Gobara ta cinye shaguna a Tashar Motoci ta Jabi a Abuja
Wani ɗan kasuwar ya ce da misalin ƙarfe 3.30 na dare wutar ta tashi, amma ba a kai ga gano musabbinta ba.
Ana fargabar shaguna kimanin 100 sun ƙone sakamakon tashin gobara da tsakar dare a Babbar Tashar Motoci ta Jabi da ke shiyyar Utakoa Abuja, a safiyar Asabar.
Da tsakar dare kafin asubahi gobarar ta tashi inda ta cinye akasarin shagunan wucin gadi na masu sayar da kayan hannu da kayan waya da kayan kicin da dangoginsu a tsakanin Babbar Kofar farko da Kofa ta Biyu da ke tashar.
Wani ɗan kasuwar ya ce da misalin ƙarfe 3.30 na dare wutar ta tashi, amma ba a kai ga gano musabbinta ba.
Tun da misalin ƙarfe 4 na Asuba ’yan kasuwa da ’yan kwana-kwaba suka yi dafifi a kasuwar domin kashe wutar.
Zuwa ƙarfe 7 na safe jami’an Hukumar Kashe Gobara sun kammala aikin shawo kan wutar sun tafi, amma Aminiya ta lura cewa wutar ba ta mutu gaba ɗaya ba.
A halin yanzu ’yan Kasuwar na ƙoƙarin kwashe kayayyakin da gobarar ba ta shafa ba.