Gobara ta cinye wani gida a lokacin da ake tafka ruwan sama
Wata shu’umar gobara da ta tashi ana cikin tafka marka-markar ruwan sama a Jihar Kuros Riba ta lakume wani gida tas kamar an share a karamar Hukumar Kalaba ta Kudu. Lokacin da Aminiya ta ziyarci unguwar da lamarin ya faru ta tarar da gidan ya zama kango.Wat makwabciyar gidan mai suna Misis Ekammbong ta shaida […]
Wata shu’umar gobara da ta tashi ana cikin tafka marka-markar ruwan sama a Jihar Kuros Riba ta lakume wani gida tas kamar an share a karamar Hukumar Kalaba ta Kudu. Lokacin da Aminiya ta ziyarci unguwar da lamarin ya faru ta tarar da gidan ya zama kango.
Wat makwabciyar gidan mai suna Misis Ekammbong ta shaida wa Aminiya cewa da misalin karfe 1:00 na rana ana tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya ne sai gidan ya kama da wuta. “Duk da ruwan sama da ake yi, amma bai hana gobarar nan cinye gidan ba,” inji ta.
Shi ma Udofia Sam ya ce “Tunda nake ban taba ganin ana ruwa ana gobara ba sai a wannan karo, amma dai kila laifi mazauna gidan ko mai gidan ya yi wa wani aka aiko masa da gobara, idan ba haka ba yaya za a ce ana tafka ruwa gida na konewa.”
Wadanda Aminiya ta zanta da su game da gobarar sun ce an kirawo jami’an kashe gobara sun yi bakin kokarinsu amma haka gidan ya kone. Mazaunan gidan sun ki cewa komai lokacin da wakilinmu ya nemi jin ta bakinsu.
A kwanan baya wani gini a unguwar Otop-Abasi ya rufta ya kashe wata mace da tsohon ciki.
Wakilinmu ya leka ofishin jami’an kashe gobara domin jin yadda suka kare da gobarar amma wani da ya nemi a sakaya sunansa ya ce sun ga abin mamaki a yayin kashe gobarar, kuma duk da sun yi bakin kokarinsu haka gidan ya kone ba tare da sun ci nasara ba. Har zuwa hada wannan labari ba a gano musabbabin aukuwar gobarar ba.