Gobara ta haddasa asarar dukiya a kasuwar Katsina

Wata gobara da ta tashi a Sabuwar Kasuwar da aka fi sani da ’Yar Kasuwa da ke cikin garin Katsina ta janyo asarar miliyoyin kudi.Ita dai wannan gobara da ta faru a sashen masu sayar da kujeru da gadaje, ta tashi ne a maraicen Alhamis. Kamar yadda mai shagon da gobarar ta faro daga wajensa, […]

Gobara ta haddasa asarar dukiya a kasuwar Katsina
Gobara ta haddasa asarar dukiya a kasuwar Katsina

Wata gobara da ta tashi a Sabuwar Kasuwar da aka fi sani da ’Yar Kasuwa da ke cikin garin Katsina ta janyo asarar miliyoyin kudi.
Ita dai wannan gobara da ta faru a sashen masu sayar da kujeru da gadaje, ta tashi ne a maraicen Alhamis. Kamar yadda mai shagon da gobarar ta faro daga wajensa, mai suna Alhaji Shehu wanda aka fi da lakanin ‘dan Alhaji A. Tausaya’ ya shaida cewa: “A kullum ina tafiya gida a lokacin da Sallar Magariba ta matso amma a wannan rana Allah bai nufe ni da tafiya gidan ba sai na tsaya a nan masallaci don in yi sallar. Gama sallar ke da wuya sai ga yaro ya nufo wajenmu a guje yana cewa, ‘wuta, gobara.’ Muka tashi da sauri domin kai dauki. Ina zuwa sai na tarar da tuni wutar ta cinye shago na daya, na biyu har ta wuce gaba. Kuma dukkan wadannan shaguna kusan goma ko sama da haka da gobarar ta cinye ko ta lalata nawa ne. Domin ina zaune a wajen nan sama da shekaru 30 da suka wuce, kusan duk wanda ka gani nan yana aiki kodai yaro ne har yanzu ko ni na koya masa aikin. Saboda muna aikin gyara da kuma yin sabbin kujeru da gadaje na katako a nan tare da sayarwa. To a yau kaddara ta fada mana.”
An dai yi hasashen ko mashaya ne suka haddasa gobarar, watakila ko ta hanyar jefar da wutar taba, domin a lokacin da wutar ta fara ci babu wutar lantarkin da ko za a yi tunani ko mayar da wuta da karfi ko wata matsala ta faru ta sanadiyarta. Mafi yawan wadanda abin ya shafa da aka zanta da su sun dogara abin da kaddara duk da cewa wasu sun nuna damuwarsu a kan irin shara da ake bari ba tare da an kwashe a cikin lokaci ba, wadda hakan a cewarsu tana iya haddasa faruwar gobarar ta ko yaya burbushin wuta ya fada a kanta.
Shi ma Sakataren kungiyar masu sayar da gadaje da kujerun katako na wannan kasuwa, Abba Ibrahim, ya shaida mana cewa, gobarar wadda ta fara tashi da misalin karfe bakwai da wasu mintoci. “Jama’a tare da ma’aikatan kashe gobara sun yi iyakar kokarinsu na ganin an kashe wannan wuta wadda ta rika hauhawa kamar ana zuba mata mai. Duk da cewa, wutar ta yi barna domin sama da shaguna 10 suka kone wanda in ba domin wancan kokari na ma’aikata da jama’a tare da taimakon Allah ba, da kasuwar baki dayanta za ta kone. Har ila yau, an samu wasu marasa imani, wadanda suka yi amfani da wannan dama ta nuna ceto ko kawo dauki, suka kwashe kayan jama’a. Domin a lokacin an yi kokarin kwashe kayan da ke cikin wasu shagunan da ake ganin gobarar na iya kai wa gare su amma kuma wani abin bakin ciki sai wannan ya zamo wata dama ce ga wasu ta daukar kayan jama’a da wata manufa ba ta taimako ba. Yanzu dai ka ga wannan shagon babu komai ciki, duk an sace su.” Inji Sakataren.
Ya yi kira ga gwamnatin jiha da wadanda Allah Ya hore ma wa da su kawo wa wadanda wannan al’amari ya shafa dauki, domin sun shiga cikin wani hali.