Gobara ta halaka mutum 11 a Ibadan

Mahukumta a Jihar Oyo, sun tabbatar da mutuwar mutane 11 da suka kone kurmus a wajen gobarar da ta rutsa da su da yammacin ranar Asabar a birnin Ibadan. Gobarar ta tashi ne a lokacin da direban wata motar tanka dauke da man fetur ya kasa shawo kanta, inda ya taho a guje kuma, ya […]

Gobara ta halaka mutum 11 a Ibadan
Gobara ta halaka mutum 11 a Ibadan

Mahukumta a Jihar Oyo, sun tabbatar da mutuwar mutane 11 da suka kone kurmus a wajen gobarar da ta rutsa da su da yammacin ranar Asabar a birnin Ibadan. Gobarar ta tashi ne a lokacin da direban wata motar tanka dauke da man fetur ya kasa shawo kanta, inda ya taho a guje kuma, ya auka a kan wasu kananan motoci da ke tsaye a unguwar Molete, wadda a nan take wuta ta tashi tana bin malalar fetur zuwa sassa daban-daban da ke kusa da wannan wuri.

Shaguna da kantunan ‘yan kasuwa fiye da 40, tare da kananan motoci da babura da sauran kadarori na miliyoyin Naira ne suka kone a wajen wannan gobarar, inda ta shafe sama da awoyi bakwai tana ci, ba tare da an shawo kanta ba. Mutane 16 da suka samu munanan raunuka ne aka garzaya da su asibitocin don ceto rayukansu.
A Lahadi ne Gwamna Abiola Ajimobi, ya jagoranci wasu jami’an gwamnati zuwa wurin da gobarar ta auku, tare da jajanta wa iyalan wadanda suka rasa rayukansu. Gwamnan wanda ya nuna matukar bakin cikinsa da aukuwar wannan al’amari, ya ce, sau da yawa ya sha bayar da shawara ga jama’a da su guji hada-hadar kasuwanci a kusa da tituna da manyan hanyoyi.
Aminiya ta gano cewa, daga cikin mutanen da wannan gobara ta rutsa da su har da wata mata da ‘ya’yanta uku da suka kone kurmus a cikin shagon da suke sayar da kayayyakin bukatun yau da kullum. Haka kuma akwai kananan motoci guda 15 da babura 12 da keke Napep mai kafa uku guda shida da kadarori da aka baje su a daidai wannan wuri mai cunkoson jama’a da abubuwan hawa. Mazaunan unguwar Molete, sun nuna cewa, sai da aka yi fiye da sa’o’i biyu wutar tana ci kafin ma’aikatan kashe gobara su kawo dauki, tare da taimakon jama’a aka shawo kanta.
Binciken ya nuna cewa, tarihin kafuwar birnin Ibadan bai samar da kebabbun kasuwanni a cikin birni mafi girma a nahiyar Afrika ba. Shi yasa mafi yawan kasuwannin ke hada-hadar kasuwanci a gefen hanyoyin mota. A wasu unguwannin ma, ‘yan kasuwan ne suke baje kolinsu a kan titunan da suke rufe su baki daya.
Ya zuwa yanzu wasu ‘yan siyasa masu sha’awar neman mukamai a Jihar Oyo, sun fara ziyartar wajen da aka yi gobarar, domin nuna alhini da jajanta wa iyalan wadanda suka rasa rayukansu, tare da bayar da tallafi.