Gobara ta halaka uwa da ‘ya’yanta hudu a Kaduna

‎Gobara ta halaka wata uwa da jariri da ‘ya’yanta uku a unguwar Rigasa da ke  karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna. Gobarar ta faru ne a daren ranar Laraba da misalin karfe 2:00 na dare. Mijin matan mai Suna Sani Yahaya Jumare, ya samu kubuta ta tagar dakin lokacin da makwabtansa suka kai masa dauki. […]

Gobara ta halaka uwa da ‘ya’yanta hudu a Kaduna

Wata Gobara

Gobara ta halaka wata uwa da jariri da ‘ya’yanta uku a unguwar Rigasa da ke  karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

Gobarar ta faru ne a daren ranar Laraba da misalin karfe 2:00 na dare.

Mijin matan mai Suna Sani Yahaya Jumare, ya samu kubuta ta tagar dakin lokacin da makwabtansa suka kai masa dauki.

Matar mai Suna Rukayya da ya’yanta uku sai kuma diyar kanwar mijinta wanda ta zo hutu gidan duk sun rasu.

An kuma yi jana’izarsu kamar yadda musulunci ya tanadar‎.