Gobara ta halaka yara biyu iyayensu na ji na gani
A ranar Alhamis din makon jiya ne mazauna Unguwar Malali da ke kusa da gidaje masu saukin kudi na Dutsin-Safe a garin Katsina suka ga wani abin tausayi inda gobara ta halaka wasu kananan yara biyu ba tare da sun iya ceto su ba.Malama Hadiza mahaifiyar yaran masu suna Ibrahim, mai shekara uku, da Muhammadu […]

A ranar Alhamis din makon jiya ne mazauna Unguwar Malali da ke kusa da gidaje masu saukin kudi na Dutsin-Safe a garin Katsina suka ga wani abin tausayi inda gobara ta halaka wasu kananan yara biyu ba tare da sun iya ceto su ba.
Malama Hadiza mahaifiyar yaran masu suna Ibrahim, mai shekara uku, da Muhammadu mai wata 11 ta ce, “muna tare da yaran da babansu a cikin daki da misalin karfe 8:30 na safe, sai aka shigo sayen itace na fita shi ma mahaifinsu ya fito, bayan na sallami mai sayen itacen Allah cikin ikonSa maimakon in koma dakin sai na shiga daya dakin ba tare da sanin abin da zan yi cikinsa ba, kwatsam sai kukan yaran na ji. Na yiwo waje, amma Allah Ya rufe mini idanu ban san inda zan nufa ba, sai wuta kawai nake gani a cikin dakina da na baro yaran suna kwance a kan gado suna barci.”
Ta ci gaba da cewa “Ina ji ina gani dakina na cin wuta ga kuma ’ya’yana biyu a ciki, amma ban iya ceto su ba saboda yadda wutar take tashi.”
Malama Hadiza ta ce, ba ta iya tantance abin da ya haddasa tashin wutar ba, domin ba ta aje komai a cikin dakin mai nasaba da wuta ba, ga shi kuma babu wutar lantarki a lokacin da wutar ta tashi tun bayan kyallo ta da aka yi aka dauke. “Duk da na yarda da kaddara, amma a matsayina na mahaifiya na ga tashin hankalin da har in mutu ba zan manta da shi ba; ga kukan ’ya’yana ina ji a cikin dakin da wuta ke ciki amma babu abin da zan iya yi har na bar jin kukansu. Amma na yi imani da kaddara kuma na yafe musu duk wani abin da suka yi mini kuma ina nema musu rahamar Allah,” inji ta.
Shi kuwa mahaifin yaran Malam Muhammadu Abbati ya ce,”a lokacin da aka shigo sayen itacen bayan Hadiza ta fita, ni ma na fita na dauki buta domin zagayawa ban-daki, amma ban san abin da zan yi ba domin na shiga koda bawali banyi ba, sai na ji kuwwarta tare da jin kukan yaran inda ni da ita muka nufo wurin dakin amma saboda irin yadda wutar ke tashi da feshi muka gaza isa. Mun ci gaba da neman daukin jama’a, ita kuma wutar na kara ruruwa tamkar ana zuba mai.”
Makwabta da suka taru don ceto yaran har fasa bango dakin suka yi daga baya domin kashe wutar da ke ci a ciki da kuma zagayen dakin amma ba su samu nasarar ceto su ba.
Mahaifan yaran sun ce da fitowarsu da tashin wutar mai kama da ana zuba mata fetur duk bai dauki tsawon minti uku ba, kuma sun tabbatar da babu wani abu da suka ajiye ko suka gani da zai iya tayar da wannan muguwar gobara ta kankanen lokaci da ta janyo mutuwar ’ya’yansu biyu da suke da su.