Gobara ta halaka yara uku a Ajah-Legas
Yara uku ’yan gida daya sun kone kurmus yayin da gobara ta tashi a dakin da suke kwance a unguwar Sasha da ke Jihar Legas. Aminiya ta gano cewa gobarar ta tashi ne a karshen makon da ya gabata sakamakon kyandir din da mahaifin yaran ya kunna a dakin da suke barci.Wani wanda ya gane […]
Yara uku ’yan gida daya sun kone kurmus yayin da gobara ta tashi a dakin da suke kwance a unguwar Sasha da ke Jihar Legas.
Aminiya ta gano cewa gobarar ta tashi ne a karshen makon da ya gabata sakamakon kyandir din da mahaifin yaran ya kunna a dakin da suke barci.
Wani wanda ya gane wa idonsa yadda lamarin ya auku ya bayyana wa Aminiya cewa mahaifin yaran ya kunna kyandir din ne a dakin da yaran suke barci, sai ya tafi asibitin da aka kwantar da mahaifiyarsu don ya duba ta sakamakon haihuwar da ta yi, kafin ya dawo sai gobarar ta tashi ta kone su kurmus.
Shugaban Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Legas ya tattabatar da aukuwar lamarin, inda ya ce wutar kyandir ce ta janyo tashin gobarar.
Ya ce: “Tuni muka kwashe gawarwakin yaran muka kai su dakin ajiyar gawa na asibitin gwamnatin Jihar Legas. Shi ya sa muke yi wa jama’a gargadi cewa su guji kunna kyandir a gidajensu kuma su rika kula sosai duk lokacin da suka kunna wuta tare da daukar matakan da suka kamata na kare yiwuwar tashin gobara. Tuni mutanenmu suka kashe wutar amma ta yi barna sosai, tunda ta kashe rayuka ta kuma kone dukiyoyi.”
Da yake jawabi, Sarkin Hausawan yankin Sasha, Malam Iliyasu Isa kira, ya ce bai taba ganin tashin hankali irin na barnar da gobarar ta yi a yankin ba. “Gaskiya tunda nake zaune a wannan yanki ban taba ganin tashin hankali irin wanda gobarar nan ta haddasa ba. Domin mutane sun shiga tashin hankali tare da jimamin rasuwar yaran, ganin cewa mahaifiyarsu ta haihu ta samu sabon jariri amma kuma sai Allah ya jarrabe su da ita da mijinta da wannan ibtila’i. Shi ya sa kodayaushe nake fadakar da jama’armu cewa su rika kula kuma suna kiyayewa da wuta musamman ma a wannan lokaci na damina a Jihar Legas.”
A wata sabuwa kuma gobara ta tashi a kasuwar saye da sayerwa da ke yankin Ajah a jihar. Kodayake jami’an Hukumar Kashe Gobara na jihar sun shawo kanta kafin ta yi wa kasuwar mummunar illa amma duk da haka sai da ta kone wasu shaguna tare da kayayyakin da ke ciki.
Wadanda lamarin ya auku a kan idonsu sun bayyana cewa gobarar ta tashi ne da yammacin ranar Lahadi sakamakon kawo wutar lantarki da aka yi.
’Yan sanda da ke kula da yankin sun tabbatar da aukuwar lamarin sai dai ba su yi karin bayani ba.